Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Sufurin Gwamnati, An Harbe Mutane
- Wasu fusatattun yan bindiga sun harbi fasinjoji uku dake tafiya a cikin motar kamfanin Benue Links kusa da garin Otukpo a daren Asabar
- Babban manajan kamfanin sufurin ya tabbatar da cewa fasinjojin suna karbar magani sannan kamfanin zai biya dukkan kudaden asibitin
- Hukumar sufurin ta sake jaddada dokar hana tafiyar dare ga dukkan direbobinta domin kaucewa fadawa tarkon yan bindiga a hanyoyin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Wasu ’yan bindiga sun harbi fasinjoji uku a daren ranar Asabar, 10 ga Janairu, 2026, yayin da suke tafiya daga garin Gboko zuwa Legas.
Fasinjojin na tafiya ne a cikin motar kamfanin sufuri mallakin jihar Benue, wadda aka fi sani da Benue Link lokacin da suka fada komar 'yan bindigar.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun harbi fasinjoji a Benue
Lamarin ya faru ne ’yan kilomitoci kafin isa garin Otukpo, inda maharan suka tare motar suka buɗe mata wuta baji ba gani, in ji rahoton Tribune.
Jami’ar yaɗa labarai ta kamfanin Benue Links, Johnson Ehi Daniel, ta tabbatar da cewa mutanen da abin ya shafa suna karɓar magani a asibitin koyarwa na Jami’ar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Otukpo.
Shugaban kamfanin, Kwamared Alexander Aondohemba Fanafa, tare da manajan kasuwanci, Edache Joseph, sun ziyarci waɗanda suka ji raunin a ranar Lahadi, 11 ga Janairu, 2025.
Kwamared Alexander Fanafa ya tabbatar wa iyalan fasinjojin cewa kamfanin zai ɗauki dukkan nauyin jinyarsu ɗari bisa ɗari tare da ba su kulawar da ta dace.
Yadda 'yan bindiga suka farmaki motar sufuri
A cewar Daniel, harin ya faru ne da misalin ƙarfe bakwai na yamma a yankin "Burnt Bricks" da ke kan hanyar Otukpo.
Motar ta bar Gboko ne da nufin kwana a Otukpo domin ci gaba da doguwar tafiyar zuwa Legas washegari, amma sai maharan suka yi mata kwanton ɓauna.
Shugaban kamfanin ya yi amfani da wannan zarafi wajen kira ga dukkan direbobin kamfanin da su kiyaye dokar hana tafiyar dare, yana mai jaddada cewa kiyaye lokaci shi ne mabuɗin tsira daga tarkon miyagun mutane.

Source: Original
An taba sace fasinjoji a motar Benue Links
Wannan harin ba shi ne na farko ba, domin a watan Yunin 2025 ma, an taɓa kai wa wata motar kamfanin hari a yankin Okpokwu inda aka yi fashi da garkuwa da mutane.
Jami’an tsaro na rundunar soji da ’yan sanda sun isa wurin da abin ya faru a cikin dare, inda suka fara sintiri na musamman a cikin dazuzzukan yankin don kamo waɗanda suka aikata wannan danyen aiki.
Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da cewa za ta tsaurara tsaro a manyan hanyoyin jihar domin tabbatar da amincin matafiya da kare su daga barazanar mahara.
An hallaka kasurgumin dan bindiga
A wani labari, mun ruwaito cewa, an tabbatar da mutuwar wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi jama'a, Terkaa Samuel a musayar wuta a jihar Benue.
Rundunar yan sanda reshen jihar Benuwai ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunta, DSP Udeme Edet ta fitar a Makurdi.
Haka zalika 'yan sanda sun kai dauki bayan samun labarin barkewar rikici tsakanin wasu 'yan daba, inda aka kama mutane takwas.
Asali: Legit.ng

