Ba a hana motocin Dangote yin tafiyan dare ba - FRSC

Ba a hana motocin Dangote yin tafiyan dare ba - FRSC

Hukumar kiyayye hadurra na kasa (FRSC) ta ce ba ta hana manyan motoccin kamfanin Dangote ko sauran masu ababen hawa yin tafiyar dare ba.

Jami'in wayar da kan al'umma na hukumar, Bisi Kazaeem ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yin karin bayani kan wani rahoton da aka ce ya fitar kan lamarin kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rahoton ya ce wai Mista Kazeem ya ce hukumarsa da kamfanin Dangote sun cimma yarjejeniya cewa motocin Dangote za su dena tafiyar dare.

Sai dai sanarwar da ya fitar ranar Laraba, Mista Kazeem ya ce FRSC ba ta taba cewa za ta hana motocin Dangote bin tituna a Najeriya daga karfe 7 na yamma zuwa 7 na safe ba.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace kujerar dan majalisa PDP a jihar Sokoto, ta bayar da umurnin yin zaben raba gardama

"FRSC ba ta ce za a kama motoccin Dangote bayan karfe 7 na yamma ba," a cewa Kazeem.

"Hukumar mu ba ta ce haka ba, anyi kuskure ne wurin cewa mun ce za mu kama motocci.

"Dama sun saba yin taro da kamfanin Dangote da wasu kamfanonin kan tsaro.

"Irin wannan taron ne mu ka yi a ranar Talata inda muka yi wasu yarjejeniya amma ba mu ce za mu rika kama motocin su ba."

Ya yi bayanin cewa FRSC ba ta da ikon kama motoci da dadare saboda babu wata doka a halin yanzu da ta hana irin wadannan motoccin yin tafiyar dare.

Ya ce abinda hukumar kawai za ta iya yi shine wayar da kan mutane kan hatsarin da ke tattare da yin tafiyar dare.

Rahotanni sun ce hukumar ta bukaci kamfanin Dangote ta rika kawar da motocinta da suka lalace kan hanya cikin gaggawa tare da tantance kwararun direbobin kafin daukansu aiki.

Mista Kazeem ya ce Boboye Oyeyemi ya bayar da umurnin saka wa dukkan motocin Dangote na'urar takaita gudu a kuma saka lambobin Najeriya a duk motoccin kafin ranar 31 ga watan Disamba.

"Kamfani Dangote ya bayar da bayanai kan duk wani direba da ya saba dokokin FRSC domin ayi masa gwajin hankali.

"Kamfanin ya bayar da sunan duk wani direba da ya tsere bayan afkuwar hatsari saboda a gano shi"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel