'Gaskiyar Dalilin da Ya Sa Buhari Ya Nada Ni Minista a 2015,' Inji Lai Mohammed
- Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa aminci da biyayya ne suka sanya Muhammadu Buhari ya nada shi minista har tsawon shekaru takwas
- Tsohon ministan ya kaddamar da littafinsa na musamman domin girmama ranar haihuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Littafin ya bankado sirrin yadda Buhari ya kira Lai Mohammed ta waya domin sanya shi a kwamitin sauyin gwamnati a shekarar 2015
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana gaskiyar dalilin da ya sanya tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari ya nada shi ministan yada labarai a shekarar 2015.
Lai Mohammed ya ce Buhari ya na da shi minista ne sakamakon amana, biyayya, da kuma doguwar hidima da ya yi wa tsohon shugaban kasar.

Source: Facebook
Lai Mohammed ya kaddamar da littafi a Abuja
Tsohon ministan ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa mai suna "Headlines and Soundbites: Media Moments that Defined an Administration," in ji rahoton Punch.
An ƙaddamar da littafin ne a Abuja ranar 17 ga Disamba, 2025, domin ya dace da ranar da ya kamata ace ta zamo ta cikar Buhari shekaru 83, amma kuma ta zo bayan ransa.
Littafin ya yi bayani dalla-dalla kan yadda Lai Mohammed ya kasance ɗaya daga cikin manyan jami’an gwamnatin Buhari na tsawon shekaru takwas.
Sannan littafin ya yi bayani kan irin alaƙar kut-da-kut da ke tsakanin Lai Mohammed da Buhari wadda ta dade har zuwa rasuwar tsohon shugaban kasar a ranar 13 ga Yuli, 2025.
Yadda Buhari ya sanya Lai Mohammed a kwamiti
Lai Mohammed ya ba da labarin yadda aka sanya shi a cikin kwamitin sauyin gwamnati ƙarƙashin Alhaji Ahmad Joda a watan Afrilun 2015.
Ya ce shugaban ƙasa da kansa ya kira shi ta waya yayin da yake Lagos, inda ya tambaye shi: “Lai, kana ina?” Bayan ya shaida masa yana Lagos, Buhari ya tambaye shi me ya sa ba zai zo taron kwamitin sauyi ba a Abuja washegari.
Lokacin da Mohammed ya sanar da Buhari cewa shi ba mamba ne na kwamitin ba, Buhari ya ce, “Ok, Tunde (Sabiu) zai kira ka,” kuma cikin kankanin lokaci aka aiko masa da wasiƙar naɗi.
Lai Mohammed ya bayyana cewa wannan kiran ya nuna irin amana da Buhari ke da ita a kansa tun kafin a naɗa majalisar ministoci.

Source: Getty Images
Doguwar alaƙar siyasar Lai da Buhari
Tsohon ministan ya bayyana cewa alaƙarsa da Buhari ta samo asali ne tun a shekarar 2012 lokacin da ya roƙi Buhari ya rubuta gabatarwa ga littafinsa na farko, "Witness to History", ta hannun Nasir El-Rufai. Buhari ya amince, har ma ya halarci taron ƙaddamar da littafin.
Bayan nan, sun ci gaba da ganawa akai-akai a lokacin da ake shirin haɗewar jam’iyyun da suka samar da APC, inda suke yin tarurrukan siyasa a Kaduna tare da Shugaba Bola Tinubu da Bisi Akande.
“Gudanar da aiki a gwamnatin Buhari ya ba ni damar ganin yadda shugaban ke kishin ƙasa da kuma yin riƙo da gaskiya.”
- Lai Mohammed.
'Dalilin toshe Twitter a lokacin Buhari' - Lai
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya ce dakatar da amfani da Twitter (X) a 2021 na ɗaya daga cikin matakai mafi nauyi da ya taɓa yanke wa.
Ya bayyana cewa tsaron ƙasa ne ya rinjayi duk wata illa da matakin zai iya haifarwa ga ’yan kasuwa da masu amfani da kafar a Najeriya.
Lai Mohammed ya ce shawarar ba ta da alaƙa da goge sakon tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, sabanin rade-radin da suka bazu a lokacin.
Asali: Legit.ng


