Yanzu-yanzu: Tsohon sakataren gwamnati, Alhaji Ahmad Joda, ya rasu
- Allah ya yiwa tsohon sakataren din-din-din rasuwa
- Alhaji Ahmad Joda ya yi dogon jinya a asibiti
- Yan Najeriya da dama sun aika sakon ta'aziyya ga iyalansa
Yola - Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Najeriya lokacin mulkin Soja kuma mutum na farko da Buhari ya ba mukami bayan nasara a 2015 , Alhaji Ahmed Joda, ya mutu.
BBC ta ruwaito daya daga cikin 'yayan marigayin, Asma'u Joda, ta bayyana cewa mahaifinta ya rsu ne yau Juma'a a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.
Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.
Alhaji Ahmed Joda ya cika ne yana mai shekaru 91 a duniya.
A cewar DT, Ahmad Joda ya rasu ne bayan jinya a asibitin FMC Yola.
Joda ya yi karatunsa a Najeriya da kuma Birtaniya inda ya halarci Kwalejin Pitmans da ke birnin London daga 1954 zuwa 1956.
Ya rike kujeran sakataren din-din-din lokacin gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon (Mai murabus).
Shugaba Buhari ya dawo gida bayan kimanin makonni biyu a Landan
Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gidan Najeriya bayan zaman ganin Likita na kimanin makonni biyu da yayi a birnin Landan, kasar Birtaniya.
Buhari ya dira a Abuja ne da yammacin Juma'a, 13 ga watan Agusta, 2021.
Mai magana da yawun shugaban kasan, Femi Adesina, ya bayyana hakan da yammacin nan a shafinsa na Facebook.
Asali: Legit.ng