Dakarun Sojojin Najeriya Sun Kara Kaimi a Yaki da 'Yan Bindiga a Jihohin Arewa 2
- Rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da manyan hare-hare a jihohin Kwara da Niger domin kakkabe 'yan bindiga da masu garkuwa
- Birgediya Janar Nicholas Rume ya bayyana cewa an kafa sababbin sansanonin soja a Patigi da Ilemona domin tabbatar da tsaro
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya jinjina wa sojoji wajen dawo da zaman lafiya tare da alkawarin cigaba da ba su goyon baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Rundunar sojojin Najeriya ta tsananta gudanar da kai hare-hare da sauran manyan ayyukan tsaro a sassan jihohin Kwara da Niger.
Sojoji sun kai hare-haren ne domin yaƙar 'yan fashin daji, masu garkuwa da mutane, da sauran 'yan bindiga da ke addabar yankin Arewa ta Tsakiya.

Source: Twitter
Sojoji sun tsananta hare-hare a Arewa
Kwamandan hedikwatar 22 Birged, Birgediya Janar Nicholas Rume, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 10 ga Janairu, 2026, yayin bukin sada zumunta na shekara-shekara (NASA) da aka gudanar a barikin Sobi da ke Ilorin, in ji rahoton Punch.
A cewar Birgediya Janar Rume, rundunar ta ƙaddamar da manyan ayyukan tsaro da nufin murƙushe 'yan ta'adda a yankunan da take kula da su.
Waɗannan ayyuka sun haɗa da hare-haren Operation Fansan Yamma, Operation Harmony, da kuma Operation Park Strike IV da V da aka kammala kwanan nan.
An kaddamar da waɗannan hare-haren ne a dajin "gandun dabbobi na Kainji" da ƙauyukansu da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Niger, da kuma yankunan Kaiama da Baruten a jihar Kwara.
Ya jaddada cewa an kafa sansanonin soja na FOBs a Patigi da Ilemona, tare da wasu sansanonin sintiri a Babasango da Gada, don murƙushe ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.
Gwamnan Kwara ya yiwa sojoji alkawari
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda Birgediya Janar Saliu Tunde Bello (mai ritaya) ya wakilta, ya yaba wa bajinta da sadaukarwar sojojin.
Gwamnan ya bayyana cewa:
“Ina jinjina wa ƙoƙarin 22 Birged da daukacin rundunar sojin Najeriya wajen fuskantar waɗannan ƙalubale. Jajircewarku wajen maido da zaman lafiya abin a yaba ne.”
Gwamnan ya sake jaddada goyon bayan gwamnatinsa wajen samar da kayan aiki ga rundunar domin dorewar zaman lafiya a jihar, yana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da sojoji ya samar da sakamako mai kyau wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
An gudanar da bikin NASA
Birgediya Janar Rume ya tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar a shirye take ta ci gaba da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro.
Bukin na NASA, wanda ke zama dandali na ƙarfafa gwiwar jami'ai da murnar al'adun Najeriya daban-daban, ya nuna irin shirin da sojojin suke da shi na fuskantar barazanar ta'addanci, fashi da makami, da garkuwa da mutane da suka addabi sassan Arewa.
Asali: Legit.ng

