Yan Bindiga Sun Tura Wasiku ga Al'umma da Turanci, Za Su Kai Hari saboda Haraji
- Rundunar ‘yan sandan Oyo ta fara bincike bayan gano wasiƙun barazana daga ‘yan bindiga zuwa ga al'umma
- An ce wasiƙun biyu sun haddasa fargaba, inda ɗaya ke cikin harshen Yarbanci, ɗaya kuma Turanci suna barazanar hari ranar 20 ga Janairu, 2026
- ‘Yan sanda sun bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, suna cewa ana gudanar da bincike mai zurfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osgobo, Oyo - Rundunar ‘yan sanda a Jihar Oyo ta tabbatar da gano wata wasiƙar barazana daga wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun rubuta wasikun ne a garin Ikoyi-Ile, cikin karamar hukumar Oriire a jihar.

Source: Original
Oyo: 'Yan bindiga sun yi barazanar kai hari
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga kakakin rundunar yan sanda a Oyo, Ayanlade Olayinka wanda ya wallafa a Facebook.
Majiyoyi sun tabbatar da yaduwar wasikun da aka ce an rubuta da yaren Turanci da kuma Yarbanci.
Tun bayan gano wasiƙar, mazauna yankin sun shiga fargaba da tashin hankali, sakamakon barazanar da ke nuni da yiwuwar kai hari nan ba da jimawa ba.
Ikoyi-Ile na daga cikin al’ummomin Oriire, yankin da aka kashe jami’an gandun daji biyar kwanan nan, kusa da wuraren yawon shakatawa.
Bincike ya nuna cewa an samu wasiƙu biyu daban-daban da ake zargin ‘yan bindiga ne suka rubuta, aka aje su a gaba da bayan wani gini a garin.
Wasiƙun sun gargadi mazauna cewa za a kai hari ranar Talata, 20 ga Janairu, 2026, lamarin da ya ƙara tsoratar da jama’a.
Ɗaya daga cikin wasiƙun, wacce aka rubuta da Yarbanci ba tare da sa hannu ba, ta kasance mai taken “Lati Odo Bandit.”
A cikin wasiƙar an rubuta cewa:
“Za mu zo ranar 20 ga Janairu, 2026. Ku jira mu, ku shirya mana. Mun zo ne domin kawo muku hari.”
Wasiƙar ta biyu kuwa an rubuta ta da Turanci, inda aka ce:
“Sanarwar yan bindiga, Ku sani, mun yi aiki kwanaki uku. Gwamnati ce ta aiko mu Ikoyi-Ile.”
Ko da yake ba a tabbatar da sahihancin wasiƙun ba, lamarin ya haddasa fargaba da tashin hankali a tsakanin al’ummar yankin.

Source: Facebook
Barazanar 'yan bindiga da martanin rundunar yan sanda
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Oyo, DSP Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa ana yi wa wanda ya gano wasiƙun tambayoyi.
Ayanlade ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa inda ya ce rundunar ta fara cikakken bincike domin gano asalin wasiƙun da kuma manufar wadanda suka rubuta su.
Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda na godiya ga hadin kan jama’a, tare da roƙon su kwantar da hankalinsu yayin da jami’an tsaro ke aiki.
'Yan bindiga sun sace fasto a Oyo
An ji cewa rundunar ‘yan sandan Oyo ta tabbatar da cewa an sace Ibukun Otesile, diyar wanda ya kafa cocin Jesus Is King Ministries a gaban gidanta.
Kungiyar CAN ta bayyana cewa an turo sakon gaggawa cikin daren Alhamis, lamarin da ya tayar da hankalin limamai da Kiristoci.
CAN ta yi kira ga rundunonin tsaro su dauki mataki cikin gaggawa tare da bukatar a tura karin jami’ai domin tabbatar da kubutar da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


