Farashin Abinci: Manoma Sun Soki Gwamnati da Rashin Adalci, Sun Shiga Ɗimuwa
- Faduwar farashin kayan abinci ta jefa manoman karkara cikin mawuyacin hali sakamakon bashin noma da tsadar kayan aiki
- Manoma sun koka cewa manufofin gwamnati sun fi fifita masu saye, yayin da suke lalata rayuwar masu samar da abinci a ƙauyuka
- Masana sun yi gargadi cewa idan aka ci gaba da haka, manoma da dama za su rage noma ko su yi watsi da harkar gona gaba ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Ga manoma da dama, musamman a yankunan karkara na Jihar Niger, lokacin girbi na bana bai zo da farin ciki ba.
Maimakon haka, ya zo da sabon ƙalubale sakamakon faduwar farashin amfanin gona da kuma tsadar kayan noma, yayin da matakan gwamnati ke fifita masu saye fiye da masu noma.

Source: Getty Images
Faduwar farashin abinci ya rikita manoma
Rahoton Daily Trust ya ce manoma da dama a ƙauyuka sun bayyana cewa suna jin kamar an manta da su a cikin tsare-tsaren tattalin arziƙin ƙasa.
A cewarsu, manufofi da dama ana tsara su ne ba tare da la’akari da halin da manoman karkara ke ciki ba, ciki har da lalacewar hanyoyi, ƙarancin kudi, rashin rumbunan ajiya da matsalar samun kasuwa.
Sai dai masana sun yi gargaɗin cewa idan wannan hali ya ci gaba, manoma da yawa za su rage noman su ko kuma su bar harkar gaba ɗaya, abin da ka iya ƙara tsananta matsalar ƙarancin abinci.
Bashi da rugujewar shirin da suka yi
Wasu manoma sun shaida cewa a yanzu suna fama da matsalar biyan basussukan da suka karɓa a lokacin shuka, inda masu bin bashi ke ɗaukar matakai masu tsauri har da kama mutane.
Sun ce yayin da farashin amfanin gona ke ƙara faɗuwa, farashin kayan da suke buƙata a rayuwa na ci gaba da hauhawa.
Manoma sun bayyana cewa burinsu bayan girbi shi ne zuwa aikin Hajji, gini ko gyaran gidaje, da sayen babura domin sauƙaƙa zirga-zirga zuwa gonaki, amma faduwar farashi ta rusa waɗannan buruka.

Source: Original
Tanadin Hajji da aure sun lalace
A wani ƙauye a Niger, manoma 17 sun samu damar biyan kujerun aikin Hajji a shekarar bara ta hanyar sayar da amfanin gona.
Sai dai a bana, babu ko mutum ɗaya daga ƙauyen da ya iya biyan kuɗin Hajji, a cewar Malam Hussaini Abdullahi daga Karamar Hukumar Gbako.
Wani jami’i a Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Niger ya tabbatar da cewa manoma kaɗan ne suka zo biyan kuɗin Hajjin 2026 idan aka kwatanta da shekarar 2025.
'Farashin Abinci zai sauko a 2026' - Tinubu
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi hasashe game da farashin kayan abinci yayIn da aka shiga sabuwar shekarar 2026.
Tinubu ya yi albishir ga yan kasa cewa za a samu raguwar hauhawar farashin kaya a shekarar, yana cewa ana iya saukowa ƙasa a 2026.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce wannan sauyi zai inganta rayuwar jama’a tare da hanzarta bunƙasar tattalin arzikin Najeriya baki ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

