Yadda 'Yan Bindiga Suka Kutsa har Fadar Sarki Suka Sace Mutane
- ’Yan bindiga sama da 20 sun kutsa kai tsaye zuwa fadar Sarkin Adanla da ke yankin Ifelodun, lamarin da ya tayar da ƙarin tambayoyi kan tsaro
- An sace ’yan gidan sarauta bakwai tare da jikkata wasu mutane biyu a daren Juma’a, 26, Disamba, 2025, yayin da ake bikin ƙarshen shekara
- Jagoran 'yan sa-kai ya ce akwai alamun cin amana a lamarin lura da yadda ’yan bindigar suka kai hari har fadar suka kuma nemi kuɗin fansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara – Jagoran 'yan sa-kai na Kwara, Olaitan Oyin-Zubair, ya bayyana yadda wasu ’yan bindiga suka kutsa kai tsaye cikin fadar Sarkin Adanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar, suka sace 'yan gidan sarki su bakwai.
Lamarin, a cewarsa, ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma a ranar Juma’a, 26, Disamba, 2025, lokacin da kimanin ’yan bindiga 20 suka mamaye al’ummar Adanla suka nufi fadar Mai Martaba Oba David Adedumoye, Elerin na Adanla Irese.

Kara karanta wannan
Harin Amurka: Shugaban ƙaramar hukuma a Binuwai ya nemi ɗauki kan karuwar ƴan ta'adda

Source: Original
A wani rahoto da Punch ta wallafa, Shugaban 'yan sa-kai, Olaitan Oyin-Zubair ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansa.
Yadda aka kai hari a fadar sarki
Shugaban 'yan banga, Oyin-Zubair ya ce ’yan bindigar sun shafe kusan awa guda suna fadar ba tare da halartar jami'an tsaro wurin ba.
Ya ce sun yi awon gaba da wayoyi da wasu kayayyaki masu daraja, tare da ɗaukar wasu kayayyakin abinci da aka tanada domin bukukuwan Kirsimeti.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigar sun kwashe har wasu tukwane da ake amfani da su a fadar, ganin cewa bukukuwan Kirsimeti sun gudana a ranar da ta gabata, kuma ana shirin wani taro a washegari.
Yawan waɗanda aka sace a gidan sarki
A cewarsa, mutane bakwai aka sace yayin harin, sannan aka jikkata mutane biyu, har zuwa ranar Laraba, 31, Disamba, 2025, babu wani labari kan inda aka kai waɗanda aka sace.
Jagoran 'yan sa-kai ya bayyana cewa ’yan bindigar sun tuntubi sarkin kansa, inda suka nemi kuɗin fansa har N300m domin sakin ’yan gidan nasa.

Source: Facebook
Ina sarkin yake a lokacin harin?
Oyin-Zubair ya ce sarkin bai kasance a fadar ba a lokacin da aka kai harin, domin ya tafi Ilorin tun da rana. Ya bar fadar da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, yayin da harin ya auku bayan sa'o'i biyu kacal.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar na tambayar inda sarki da uwargidansa suke, abin da ke nuna cewa sun san mutanen da suke nema tun farko.
Jagoran 'yan sa-kai ya ce lamarin na da matuƙar rudani, domin ɗaya daga cikin ’yan bindigar na iya nuna takamaiman mutanen da za a bari da waɗanda za a sace.
Ya bayyana cewa mutumin da ke nuna mutanen na iya magana da harshen Yarbanci, amma Yarbançinsa bai yi ƙwari ba, abin da ya sa ake zargin cewa dan yankin ne.
Sarkin Musulmi ya yi magana kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana game da halin rashin tsaro da ake ciki a wasu jihohin Najeriya.
Sultan ya yi tir da kisan mutane da aka yi a kasuwar Neja, tare da kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci wajen da aka kai harin.
Ya kuma yaba da matakan da dakarun sojin Najeriya da sauran jami'an tsaro ke dauka wajen yaki da 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

