Gwamna Ya ba da Umarni a Rufe Asibitin Kwararru, An Daina Karbar Marasa Lafiya

Gwamna Ya ba da Umarni a Rufe Asibitin Kwararru, An Daina Karbar Marasa Lafiya

  • Gwamnatin jihar Taraba ta ba da umarnin rufe asibitin kwararru dake Jalingo na dan lokaci domin ba yan kwangila damar yin gyare-gyare
  • Kwamishinan lafiya ya bayyana cewa matakin ya zama dole saboda hadarin muhalli dake tattare da ayyukan gine-ginen da ake gudanarwa
  • Sai dai, wani bincike ya nuna cewa marasa lafiya da ke wankin koda sun shiga tashin hankali saboda rashin wurin da za su je wankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Taraba - Gwamnatin jihar Taraba ta ba da umarnin dakatar da dukkan ayyuka a babban asibitin kwararru na jihar da ke Jalingo na ɗan wani lokaci.

Wannan mataki ya biyo bayan amincewar Gwamna Agbu Kefas, wanda ya bayyana cewa gine-gine da garambawul ɗin da ake yi wa asibitin na tattare da haɗarin muhalli da kuma barazana ga lafiyar masu jinya da ma’aikata.

Gwamnatin Taraba ta ba da umarnin rufe asibitin kwararru na jihar don kammala gyare-gyare.
Wani dakin kwantar da marasa lafiya a asibiti. Hoto: NEWSPOINTER
Source: UGC

Gwamna ya rufe asibitin kwararru a Taraba

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Bordiya Buma, ya bayyana hakan a cikin wata takarda da ya sanya wa hannu ranar 8 ga Janairu, 2026, aka raba a Jalingo, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Dalilan da suka jawo sabon rikici tsakanin Fubara da Wike

Dr. Bordiya Buma ya umurci shugaban asibitin kwararrun da ya tabbatar da an dakatar da dukkan ayyuka domin ba wa ’yan kwangila damar gudanar da aikinsu cikin sauri ba tare da wani cikas ba.

Takardar ta bayyana cewa:

“Biyo bayan gagarumin gyara da ake yi wa asibitin, Gwamna Agbu Kefas ya ba da umarnin dakatar da ayyuka a cikinsa domin ba ɗan kwangila da mutanensa damar yin aiki cikin sauri.”

Wannan matakin ya zo ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jiha na zamanantar da fannin kiwon lafiya, kodayake mahukunta ba su fadi takamaiman ranar da za a sake buɗe asibitin ba.

Sanarwar kwamishinan ta ba da tabbacin cewa za a dawo da ayyuka da zaran an kammala gyare-gyaren da ake yi a asibitin.

Halin da ake ciki a asibitin kwararrun

Duk da wannan umarni, binciken da wakilan kafar yaɗa labarai ta News Pointer suka gudanar ya nuna wani yanayi na damuwa a asibitin kwararrun.

Maimakon kwashe kowa daga asibitin, an tarar da marasa lafiya da dama har yanzu suna kwance a bangarori daban-daban, wasu ma suna cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

NLC ta yi wa Tinubu barazana saboda a dakatar da dokokin haraji

Mafi tashin hankali shi ne halin da marasa lafiya masu wanke ƙoda suke ciki, waɗanda aka tarar da su a cikin fargaba da rashin tabbas.

Gwamna Agbu Kefas ya ba da umarni a rufe asibitin kwararru na jihar Taraba.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya na jawabi a taron majalisar SEC a Jalingo. Hoto: @GovAgbuKefas
Source: Twitter

Masana sun gargadi gwamnatin Taraba

Wanke ƙoda aiki ne da ke buƙatar tsayayyen lokaci, kuma duk wani tsaiko na iya kaiwa ga asarar rai, kamar yadda jaridar ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Wani babban ƙalubalen shi ne asibitin tarayya (FMC) da ke Jalingo, wanda ake kyautata zaton zai karɓi waɗannan marasa lafiya, a halin yanzu yana fama da matsalar lalacewar injinan wanke ƙoda da kuma ƙarancin gadaje.

Masana kiwon lafiya sun nuna fargabar cewa rufe asibitin kwararrun, wanda shi ne mafi girma a jihar, na iya haifar da mummunan sakamako idan ba a samar da ingantaccen tsarin jigilar marasa lafiya zuwa asibitoci makwabta ba cikin gaggawa.

Kotu ta hana likitoci shiga yajin aiki

A wani labari, mun ruwaito cewa, kotu a Abuja ta dakatar da kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki daga shiga yajin aiki a mako mai zuwa.

Mai shari'a E. D. Subilim ya bayar da wannan umarni ne bayan gwamnatin tarayya ta shigar da korafi domin hana likitocin janye ayyukansu.

Likitocin sun yi barazanar fara yajin aikin ne saboda zargin rashin gaskiyar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a bara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com