Bayan Mutuwar Buhari, Tinubu Ya Ware wa Tsofaffin Shugabannin Najeriya N2.3bn
- Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 2.3 a kasafin shekarar 2026 domin biyan hakkokin tsofaffin shugabannin kasar Najeriya
- Wadanda za su ci gajiyar kudin sun hada da tsofaffin shugabannin farar hula da na mulkin soja, da mataimakansu, irinsu Atiku Abubakar
- An kuma ware wasu biliyoyin kudi domin allamar tsofaffin shugabannin ma'aikata, manyan sakatarori da shugabannin hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ware zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 2.3 a cikin kasafin kuɗin 2026 domin biyan haƙƙoƙi da alawus-alawus na tsofaffin shugabannin Najeriya da mataimakansu.
Wannan bayani yana ƙunshe ne a cikin takardar kasafin kuɗin 2026 arƙashin sashen da aka yi wa laƙabi da "Hakkoƙin tsofaffin shugabannin kasa da mataimakansu."

Source: Twitter
An ware N2.3bn don tsofaffin shugabannin kasa
Mai tallafawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta fuskatar kafofin sada zumunta na zamani, Dada Olusegun ne ya wallafa bayani kan kudin a shafinsa na X.
A sakon da ya wallafa a ranar Juma'a, 9 ga watan Janairu, 2026, Olusegun ya ce:
"Gwamnatin tarayya ta ware N2.3bn a kasafin 2026 domin biyan hakkoki da alawus alawus na tsofaffin shugabannin dimokuradiyya da na mulkin soja tare da mataimakansu.
"Wannan kudi ya hada da fansho, alawus da kuma hakkokin da ake baiwa manyan tsofaffin jami'an gwamnati da ke a karkashin dokar Najeriya."
Tsofaffin shugabannin da za a kashewa N2.3bn
Wannan kasafi ya haɗa da tsofaffin shugabannin farar hula da na soja, inda waɗanda za su ci gajiyar kuɗin suka haɗa da Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, Janar Ibrahim Babangida, Janar Yakubu Gowon, da Janar Abdulsalami Abubakar.
Haka kuma, tsoffin mataimakan shugaban ƙasa irin su Atiku Abubakar, Namadi Sambo, da Yemi Osinbajo, har ma da Okoh Ebitu Ukiwe wanda ya yi aiki a zamanin mulkin soja, duk suna cikin jerin waɗanda aka ware wa wannan maƙudan kuɗi.

Source: Twitter
Sauran manyan ma’aikatan da suka yi ritaya
Baya ga tsofaffin shugabannin, kasafin na 2026 ya kuma ware maƙudan kuɗaɗe ga sauran manyan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya.
Gwamnatin ta ware Naira biliyan 24.79 domin biyan haƙƙoƙin tsofaffin shugabannin ma’aikata da manyan sakatarori. Haka kuma, an ware Naira biliyan 1 a matsayin kuɗin sallama ga tsofaffin shugabannin hukumomin gwamnati.
Wannan kasafi na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki, hauhawar farashin kaya, da kuma cire tallafi, a cewar rahoton TV 360 Nigeria.
Ko da yake hukumar RMAFC ce ke kayyade waɗannan kuɗaɗe bisa doka, kwararru na ganin akwai buƙatar rage raɗaɗin kashe kuɗi a fannin siyasa domin samar da dorewar tattalin arziƙi a ƙasa.
Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin 2026
Tun da fari, mun ruwaito cewa, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2026 ga majalisar dokokin tarayya a Abuja.
Tinubu ya gabatar da kasafin 2026, wanda ake sa ran zai lakume Naira tiriliyan 58.18 a gaban zaman hadin guiwar majalisar tarayyar a ranar 19 ga Disamba, 2025.
Shugaban kasar ya ce an ware Naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da ayyukan ci gaba, yayin da aka ware Naira tiriliyan 15.25 a matsayin kudin tafiyar da gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

