Kotu Ta Nemi a Cafke Jami’in SSS kan Sace 'Yar Yarinya, Ya Canza Mata Addini Ya Aure

Kotu Ta Nemi a Cafke Jami’in SSS kan Sace 'Yar Yarinya, Ya Canza Mata Addini Ya Aure

  • Wata kotun Majistare da ke zamanta a Jigawa ta bayar da umarnin cafke wani jami’in SSS kan zargin sace 'ar kankanuwar yarinya a Jigawa
  • Ana zargin jami'in mai suna Ifeanyi Festus ya tilasta wa wata yarinya mai suna Walida AbdulHadi sauya addini tare da yi mata fyade har ta haifi ɗa
  • Kotun ta umarci a kwato yarinyar daga hannun Festus, tare da mayar da ita hannun iyayenta gabanin a ci gaba da shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa – Wata kotun majistare a jihar Jigawa ta bayar da sammacin kama Ifeanyi Festus, wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (SSS), bisa zargin sace wata yarinya ‘yar ƙanana mai suna Walida Abdulhadi.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin Festus ya sace Walida ne daga karamar hukumar Hadejia da ke jihar Jigawa kafin ya yi awon gaba da ita.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi watsi da hukuncin kotu game da shugabancin jam'iyyar a Kano

Kotu na neman jami'in SSS ruwa a jallo
Taswirar jihar Jigawa inda aka sace yarinya mai karancin shekaru Hoto: Legit.ng
Source: Original

Premium Times ta wallafa cewa ana zargin Festus da sace Walida tun tana ‘yar shekara 16, tilasta mata sauya addininta daga Musulunci zuwa Kiristanci.

Kotu na son a kamo jami'in SSS

The Cable ta wallafa cewa an shigar da jami'in SSS a gaban kotu bisa zargin cin zarafinta ta hanyar lalata, lamarin da kai ga ta samu juna biyu har ta haife jariri.

Lauyan mai ƙara, Kabiru Adamu, ya gabatar da ƙorafi a gaban kotu inda ya nemi a tilasta cafke wanda ake zargi domin a bincike shi kan zargin da ake masa.

A cewarsa, ƙorafin ya dogara ne da tanade-tanaden Sashe na 125 da Sashe na 102(5) na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuffuka (ACJL) ta Jihar Jigawa.

Ana zargin jami'in ya sace yarinyar a Hadeja
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi Hoto: Umar Namadi
Source: Twitter

Bayan sauraron ƙorafin, Majistare Sadisu Musa ya amince da buƙatar, tare da ba da umarnin ga rundunar ‘yan sandan jihar da su cafke Festus su kuma gudanar da bincike a kansa,

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An tabbatar da mutuwar kasurgumin 'dan bindiga a Najeriya

Haka kuma, kotun ta umarci Hukumar SSS da ta gaggauta sakin Walida tare da haɗa ta da iyalanta ba tare da tsaiko ba, domin kare haƙƙinta da lafiyarta.

Ana zargin jami'in SSS da sace Walida

Rahotanni sun nuna cewa Walida ta ɓace ne shekaru da dama, lamarin da ya jefa iyalanta cikin matsananciyar damuwa.

Mahaifinta ya bayyana wa manema labarai cewa sun shafe shekaru suna neman ‘yarsu, har ma suka kai ga ɗaukar cewa ta mutu.

A cewarsa, ɓacin ran ɓacewar Walida ya jawo mutuwar mahaifiyarta, sai kwanan nan ne aka gano Walida a gidan wanda ake zargi da ke Abuja, inda aka ce ta shafe tsawon lokaci tana tsare a can ba bisa ƙa’ida ba.

Wani lauya a cikin masu bin shari’ar, Barista Hussaini, ya bayyana cewa bayan riƙe Walida na tsawon shekaru, ana zargin Festus da tilasta mata sauya addini, kuma yana neman a aura masa ita.

Barista Hussaini ya ce ya rubuta takardar ƙorafi zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Hukumar SSS, yana neman a tabbatar an gudanar da shari’ar cikin gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

An 'sace' wani hadimin gwamnan Zamfara, ana zargin akwai sa hannun Nuhu Ribasu

Zuwa safiyar Juma’a, ba a samu martani daga Hukumar SSS ba dangane da umarnin kotu ko zarge-zargen da ake yi wa jami’inta.

SSS ta karyata tsare mutane barkatai

A baya, kun samu labarin cewa Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta zargin cewa ta tsare daruruwan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba bisa umurnin wasu manyan mutanen Najeriya.

Kamar yadda aka ruwaito, hukumar ta musanta hakan ne lokacin da take mayar da martani kan wani rubutun ra'ayi da wata jarida ta buga inda aka yi zargin cewa suna tsare bayin Allah ba bisa ka'ida ba.

Mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, 2021 ya bayyana zargin a matsayin rashin fahimta da tunzura mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng