Hukumar DSS ta karyata zarginta da ake na tsare mutane ba bisa ka'ida ba

Hukumar DSS ta karyata zarginta da ake na tsare mutane ba bisa ka'ida ba

  • Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta karyata daukar umarni daga wasu daidaikun mutane
  • Ta ce tana bin ka'ida da tsarin aiki wanda akansu dukkan ma'aikatanta suka ginu kuma suke kai
  • Hukumar ta yi kira ga kafofin yada labarai da su zama masu yada abubuwan da ka iya hada kan kasa

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta zargin cewa ta tsare daruruwan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba bisa umurnin wasu manyan mutanen Najeriya.

Kamar yadda aka ruwaito, hukumar ta musanta hakan ne lokacin da take mayar da martani kan wani rubutun ra'ayi da wata jarida ta buga inda aka yi zargin.

Mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, ya bayyana zargin a matsayin rashin fahimta da tunzura mutane, ya kuma bukaci mai maganar ya janye ikirarin.

Hukumar DSS ta karyata zarginta da ake da bin umarnin 'yan siyasa
Jami'in hukumar tsaro ta farin kasa (DSS) | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Legit Hausa ta tattaro daga jaridar The Nation inda Afunanya yake cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta gargadi matasan Najeriya cewa ya kamata su rage son kudi

“Wannan ba gaskiya bane. Ba na magana a madadin 'yan sanda amma ya tabbata cewa babu wani dan Najeriya ko wani a wannan lamarin da ke hannun SSS/DSS a kan umarnin na mutane masu zaman kansu ko wasu mutane. Hukumar SSS tana da Tsarin Aiki (SOP) akan hukumar shari'ar masu laifi."

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Afunanya ya shawarci kafafen yada labarai da su kiyaye hadin kan kasar nan.

Ya ce hukumomin tsaro a kasar nan suna mutunta hakkokin ‘yan kasa kuma suna kokarin gudanar da harkokin su bisa doka.

Kotu ta hana gwamnatin Buhari da DSS SU kame Sunday Igboho

Mai shari’a Ladiean Akintola na babbar kotun Oyo ya hana hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da babban lauyan gwamnatin tarayya kamawa, bincika, tursasawa, da toshe asusun banki na Cif Sunday Adeyemo aka Sunday Igboho, The Nation ta ruwaito.

An bayar da wannan umurnin ne bayan wani tsohon kudiri da lauyansa Cif Yomi Aliu (SAN) ya gabatar a kotun a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Amurka ba ta da ikon kame Kyari, hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta yi martani

Wannan ya samo asali ne daga kudirin neman diyyar Naira biliyan 500 saboda mamaye gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar 1 ga watan Yuli.

Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa wani lokaci, zai ci gaba da zama a DSS

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta dage shari’ar Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar tsageru IPOB saboda gazawar Gwamnatin Najeriya na gurfanar da shi a gaban kotu ranar Litinin, in ji Channels Tv.

Lokacin da aka dago batun, lauya mai gabatar da kara, M. B. Abubakar, ya sanar da kotu cewa an shirya sauraren karar kuma a shirye suke su ci gaba.

Amma lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor, ya sanar da kotu cewa akwai karar da ake jira a gaban kotu don a sauya Kanu daga tsarewar hukumar DSS zuwa cibiyar gyaran hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.