Gobara Ta Kona Babban Masallaci Mai Shekaru 134, Musulmai Sun Nemi Agajin Gwamna
- Manyan shugabannin Musulmi a Lagos sun roki Gwamna Babajide Sanwo-Olu da ya jagoranci sake gina masallacin da gobara ta kone
- Masallacin da ake kira Shitta-Bey mai shekaru 134 ya gamu da iftila'in gobara wacce ta lalata a makon da ya gabata a Lagos
- Sun bayyana lalacewar masallacin a matsayin babbar asara ga Musulmi, Jihar Lagos da kuma tarihi a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Shugabannin Musulmi a Jihar Lagos sun roki Gwamna Babajide Sanwo-Olu alfarma bayan gobara ta kone masallaci.
Musulman sun roke Sanwo-Olu da ya dauki matakin gaggawa wajen jagorantar sake gina tsohon Masallacin Shitta-Bey.

Source: Getty Images
An nemi agajin gwamna bayan gobara a masallaci
Rahoton Daily Trust ya ce hakan ya biyo bayan mummunar gobara ta lalata masallacin tare da rushe Ginin Great Nigeria Insurance (GNI) da wasu gine-gine a titin Nnamdi Azikiwe.
Kiran ya fito ne a hadin gwiwa daga Majalisar Jamu’atul Muslimeen (Kwamitin Zartarwa na Babban Masallacin Lagos) da kuma kwamitin Bashorun na Yankin Olowogbowo, inda suka bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi.
A cikin wata wasika da suka aikewa gwamnan, tare da kwafin zuwa Mataimakin Gwamna, Dakta Obafemi Hamzat, shugabannin sun bukaci Gwamnatin Jihar Lagos da ta jagoranci aikin sake gina masallacin.
Sanarwar ta ce:
“Da zuciya mai cike da bakin ciki muke sanar da Mai Girma Gwamna game da lalacewar Masallacin Shitta-Bey (Moshalashi Shitta-Bey), sakamakon gobarar da ta kone Ginin Great Nigeria Insurance da wasu kadarori a titin Nnamdi Azikiwe.”

Source: Original
Tarihin masallacin da ya kone a Lagos
An gina Masallacin Shitta-Bey ne a shekarar 1891, kuma ana daukarsa a matsayin masallaci na farko a Najeriya da ya samu karbuwa a duniya bisa tsarin zamani.
Masallacin ya shahara da tsarin gine-ginen Brazil da Portugal, kuma fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon al’umma, Cif Muhammad Shitta-Bey, wanda aka fi sani da William Shitta, ne ya dauki nauyin gina shi gaba daya.
Bikin bude masallacin a ranar 4 ga Yulin 1891 ya samu halartar gwamnan Lagos na wancan lokaci, Sir Gilbert Carter, tare da wakilai daga Turkiyya da Liverpool, cewar ThisDay.
A wannan rana ne aka ba Cif Shitta lakabin “Bey” a madadin Sarkin Daular Usmaniyya, a matsayin karramawa ga gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa Musulunci.
Baya ga wannan masallaci, Cif Shitta-Bey ya sake gina Babban Masallacin Lagos a shekarar 1873, inda ya maye gurbin tsohon tsarin laka da aka yi.
An karrama shi a matsayin Seriki Musulmi na farko a Lagos, sannan daga baya aka ba shi mukamin Baba Ajo na biyu, wanda daidai yake da mukamin Baba Adinni a yau.
Malaman Musulunci na duniya sun hadu a Najeriya
An ji cewa dubban malaman Musulunci daga kasashe daban-daban sun taru a Lagos domin tattauna batutuwan zaman lafiya da tarbiyya a duniya.
Taron na duniya karo na 17 na Daaru Na’im Academy ya jawo manyan malamai, shugabanni da masana daga Afirka, Asiya, Turai da Amurka.
Tattaunawa na mayar da hankali kan kalubalen zamani da ke fuskantar al’ummomin Musulmi da hanyoyin magance su bisa ilimi da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

