Tofa: Jagororin APC Sun Taso Tinubu a gaba, Suna So Ya Tsige Ministan Abuja
- Sakataren jam'iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru ya nemi Nyesom Wike ya yi murabus daga mukaminsa na ministan Abuja
- Sanata Basiru ya tunatar da Wike cewa goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu ba shi ne zai ba shi lasisin yin yadda ya so ba
- A hannu daya, wasu jagororin APC sun gudanar da zanga zanga a Abuja, inda suka bukaci Tinubu ya tsige Wike daga minista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da ya yi murabus.
Sanata Ajibola Basiru ya nemi Nyesom Wike ya ajiye aikinsa na ministan Abuja nan take domin ya fuskanci "harkallar siyasar" jihar Rivers da ya sanya a gaba.

Source: Twitter
Rikicin Ministan Abuja da Sakataren APC
Wannan na zuwa ne bayan wata cacar baki da ta faru tsakanin manyan jiga-jigan biyu kan rikicin siyasar jihar Neja Delta, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito,
Basiru ya ne ya fara gargaɗar mataimakin shugaban APC na shiyyar Kudu-maso-Kudu, Victor Giadom, da ya daina cin mutuncin Gwamna Sim Fubara domin faranta wa Wike rai.
Wike, wanda ya yi fushi da katsalandan ɗin Basiru, ya gargaɗi sakataren jam'iyyar da ya fita daga maganar jihar Filato yayin wata ziyara da ya kai ƙaramar hukumar Oyigbo.
Sai dai Basiru ya mayar da martani da cewa Wike ba dan APC ba ne, don haka ba shi da ikon tsoma baki a harkokin jam'iyyar ko ƙoƙarin cusa manufar PDP a cikinta.
An bukaci Bola Tinubu ya tsige Wike
A ranar Laraba, 7 ga Janairu, 2026, ƙungiyar jagororin APC ta ALF da kuma takwararta ta Tinubu/Shettima Solidarity Movement sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin Abuja.
Jagororin jam'iyyar ta APC sun gudanar da zanga-zangar ne suna neman Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sauke Nyesom Wike daga muƙaminsa na minista, in ji wani rahoto Reuben Abati.
A cewar kungiyoyin, Wike ya kasance yana da girman kai, yana nuna rashin biyayya ga shugabannin jam'iyya, da kuma ayyukan da ke barazana ga haɗin kan ƙasa.

Source: Facebook
'Wike zai rarraba kawunan 'yan APC'
A cikin wata wasiƙar da suka miƙa wa Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ƙungiyoyin sun zargi Wike da sukar Sanata Ajibola Basiru, ba gaira ba dalili.
Sun bayyana cewa halayyar Wike tana neman rarraba kawunan ’ya’yan jam’iyyar APC tare da janyo rikici a yankin Neja Delta.
A cewarsu jagororin na APC, kodayake Wike ya taimaka wa Tinubu a zaɓen 2023, hakan ba zai ba shi damar cin mutuncin shugabannin jam’iyyar da ya ƙi shiga ba.
'Wike zai ci amanar Tinubu' - Jigon PDP
A wani labari, mun ruwaito cewa, Emmanuel Ogidi, ya zargi APC da ƙarfafa wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike gwiwa don rusa yan adawa.
Sai dai Ogidi wanda jigon PDP ne, ya bayyana imanin cewa nan ba da jimawa ba Wike zai iya juyawa jam’iyya mai mulki baya tare da yi mata lahani.
Sannan ya ƙara da cewa duk abin da Wike ya yi, zai iya dawowa ya shafi APC ɗin kanta, kuma za ta iya samun matsala saboda haka musamman a zabukan 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


