Manyan 'Yan Siyasa a Najeriya da Suka Fuskanci Shari'a tare da 'Ya'yansu

Manyan 'Yan Siyasa a Najeriya da Suka Fuskanci Shari'a tare da 'Ya'yansu

FCT, Abuja - Wasu manyan 'yan siyasa a Najeriya sun fuskanci shari'a tare da 'ya'yansu a kotuna daban-daban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta gurfanar da mutanen kan zarge-zargen da suka danganci satar kudin jama'a.

Sule Lamido ya fuskanci shari'a tare da 'ya'yansa
Tsohon ministan Shari'a, Abubakar Malami, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed Hoto: Abubakar Malami SAN, Sule Lamido, Senator Bala Mohammed
Source: Facebook

'Yan siyasar da EFCC ta gurfanar tare da iyalansu

Legit Hausa ta tattaro manyan 'yan siyasan da suka fuskanci shari'a tare da iyalansu kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Manyan 'yan siyansan dai sun hada da tsofaffin gwamnoni, ministoci wadanda ake zargin sun hada baki da iyalansu wajen aikata rashin gaskiya.

Ga jerinsu a nan kasa:

1. Sule Lamido da ’ya’yansa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, na ɗaya daga cikin manyan ’yan siyasa na farko da aka kama tare da ’ya’yansa bisa zargin cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

An kira sunan Atiku da aka lissafa 'yan siyasar da suka 'ruguza' jam'iyyar PDP

Hukumar EFCC ta kama ’ya’yansa biyu, Aminu Lamido da Mustapha Lamido, bisa zargin almundahanar kuɗi har Naira biliyan 10, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.

An kama su tare da yi musu tambayoyi a hedikwatar EFCC da ke Abuja, inda jami’an bincike suka gudanar da bincike mai zurfi a kansu.

Rahotanni sun nuna cewa sama da Naira biliyan 10 an tura su daga asusun gwamnatin Jihar Jigawa zuwa wasu asusu da Sule Lamido da ’ya’yansa ke da hannu a ciki daga shekarar 2007.

EFCC ta taba gurfanar da Sule Lamido
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Source: Twitter

EFCC ta ce ta gano cewa kuɗaɗen sun shiga kamfanoni 10 inda Lamido da ’ya’yansa ke matsayin daraktoci kuma su ne masu sa hannu a asusun.

Sule Lamido jigo ne a jam’iyyar PDP, kuma ya taɓa zama Ministan harkokin waje a zamanin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo, sannan ya kasance ɗan majalisar wakilai a Jamhuriya ta byu.

Ya mulki Jigawa daga 2007 zuwa 2015, kuma yana daga cikin manyan shugabannin adawa a PDP.

Sai dai a hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke karkashin jagorancin Adamu Waziri, ta yi watsi da shari'ar wadda hukumar EFCC ta shigar a kansu.

Kara karanta wannan

Kotu ta nemi cafke jami’in SSS kan sace 'yar yarinya, ya canza mata addini ya aure

Kotun daukaka karar ta ce bai kamata kotun farko ta saurari shari’ar ba domin laifuffukan ba su cikin yankin huruminta.

Ta ce ya kamata a shigar da karar a jihar Jigawa, inda aka ce laifuffukan sun faru.

2. Musiliu Obanikoro da ’ya’yansa

An zargi tsohon karamin Ministan tsaro, Musiliu Obanikoro, da karkatar da kusan Naira biliyan 4.7 daga kuɗaɗen sayen makamai da aka ware domin yaki da ta’addanci a Najeriya.

Hukumar EFCC ta gano cewa wasu daga cikin kuɗaɗen sun shiga asusun kamfanin Sylvan McNamara Limited, wanda ’ya’yansa biyu, Ibrahim Babajide da Gbolahan Olatunde Obanikoro ke da hannun jari a ciki.

Rahotanni sun ce Obanikoro ya amsa wa EFCC cewa ya ɗauki Naira miliyan 800 daga cikin kuɗaɗen ta hanyar amfani da kamfanin ’ya’yansa.

Obanikoro ya kasance jigo a gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, kuma ya yi takarar gwamnan jihar Legas a karkashin jam'iyyar PDP.

3. Murtala Nyako da ɗansa

An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, da ɗansa Abdulaziz Nyako, bisa zargin almundahanar kuɗi har Naira biliyan 29.

Kara karanta wannan

2027: Ana kulla wa EFCC makarkashiya, hukumar ta fallasa shirin ƴan adawa

Jaridar Vanguard ta ce zarge-zargen sun haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, cin zarafin mukami, buɗe asusu da dama a bankuna, da satar kuɗi.

Hukumar EFCC ta gurfanar da M
Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako Hoto: Hon Bash
Source: Facebook

EFCC ta ce sun buɗe sama da asusun banki 30 a Zenith Bank tsakanin 2011 zuwa 2013, inda aka ajiye kuɗaɗen.

4. Bala Mohammed da ɗansa

Hukumar EFCC ta tuhumi tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, da cin hanci tare da ɗansa Shamsudeen Bala.

Hukumar EFCC ta taba gurfanar da Bala Mohammed a kotu
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Bala Mohammed ya shiga Majalisar Dattawa a 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar ANPP, sannan daga baya Shugaba Goodluck Jonathan ya naɗa shi Minista bayan rasuwar Shugaba Umaru Musa Yar'adua.

EFCC ta shigar da tuhume-tuhume guda biyar a kansa, amma daga baya aka janye su, jaridar The Sun ta kawo labarin.

Sai dai, an gurfanar da ɗansa Shamsudeen gaban kotun tarayya a Abuja bisa zargin almundahanar Naira biliyan 1.1, tare da wasu kamfanoni huɗu bisa tuhume-tuhume guda 15 na safarar kuɗi.

5. Attahiru Bafarawa da ɗansa

EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, dangane da badakalar sayen makamai da ta shafi tsohon NSA, Sambo Dasuki.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari 'wurin shakatawa' na gwamnatin tarayya

Bafarawa ya mulki Sokoto daga 1999 zuwa 2007, kuma ya taɓa zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar DPP a 2007.

Jaridar The Punch ta ce an kama shi bisa zargin wanke kuɗi sama da Naira biliyan 4.1, yayin da aka kama ɗansa Sagir Bafarawa tun da farko, bisa zargin ya karɓi kuɗin a madadin mahaifinsa.

Daga baya, babbar kotun jihar Sokoto ta sallami Bafarawa da wasu mutane biyu daga tuhume-tuhume 22, bayan kotu ta ce EFCC ta kasa tabbatar da laifuffukan da ake zarginsu.

6. Bello Halliru da ɗansa

An gurfanar da tsohon Ministan tsaro, Bello Halliru, tare da ɗansa Abba Halliru bisa zargin karɓar Naira miliyan 600 daga badakalar sayen makamai, jaridar Premium Times ta kawo labarin.

Bello Halliru ɗan jihar Kebbi ne kuma tsohon shugaban hukumar Kwastam, tsohon Ministan sadarwa, kuma daga baya ya zama Shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Hukumar EFCC ta ce Abba ya karɓi kuɗin ne a matsayin wakilin kamfanin Bam Properties Limited, yayin da mahaifinsa ke da hannu a karkatar da kuɗaɗen makamai.

7. Hadi Sirika da 'yarsa

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki kauyuka cikin dare, an yi awon gaba da mutane a Katsina

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, 'yarsa Fatima da surukinsa Jalal Hamma a gaban kotu.

EFCC ta gurfanar da mutanen uku ne tare da wani kamfani mai suna Al-Duraq Investment Limited, bisa zargin almundahanar kuɗi har Naira biliyan 2.7.

Hukumar ta ce sun aikata waɗannan laifuffuka ne a lokacin da Sirika ke rike da mukamin Minista a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

8. Abubakar Malami da iyalansa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami tare da dansa da matarsa a gaban kotu.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Abubakar Malami a gaban kotu
Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami, SAN
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce EFCC ta gurfanar da shi ne tare da dansa Abdulaziz da matarsa Asabe, wadda aka bayyana a matsayin ma’aikaciya a kamfanin Rahamaniyya.

An gurfanar da mutanen ne bisa zargin karkatar da kudin jama’a da yawansu ya kai kusan Naira biliyan 9.

Kotu ta ba da belin Abubakar Malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami.

Kara karanta wannan

Nentawe: Shugaban APC ya kausasa harshe kan hare haren 'yan ta'adda a Neja

Babbar kotun karkashin jagorancin mai shari'a, Emeka Nwite ta bayar da belin Abubakar Malami, tare da matarsa da dansa, inda ta gindaya sharuda masu tsauri kafin su samu ‘yanci.

Mai shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin bayar da belin, inda ya ce kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma zai bayar da Naira miliyan 500 a matsayin beli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng