Dangote, NNPCL Sun Sauke Farashin Fetur yayin da Dala Ta Karye zuwa Kasa da ₦1420

Dangote, NNPCL Sun Sauke Farashin Fetur yayin da Dala Ta Karye zuwa Kasa da ₦1420

  • Darajar Naira ta tashi zuwa N1,418.26/$1 a kasuwar gwamnati, wani babban ci gaba da kudin Najeriyar ya samu a cikin sabuwar shekara
  • Tun daga farkon 2026, Naira ta ke ƙara daraja kan Dala inda ta samu ƙaruwar kusan N17 tsakanin watan Disambar 2025 zuwa Janairun 2026
  • Wannan na zuwa ne yayin da matatar Dangote da kamfanin mai na NNPCL suka sauke farashin da suke sayar da litar man fetur a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Naira ta kara samun karfi tare da zuwa matsayi mafi girma da ba a taɓa gani ba na N1,418.26/$ a kasuwar canjin kuɗi ta gwamnati a rana ta huɗu ta kasuwanci a sabuwar shekara.

Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da matatar Dangote ta rage farashin fetur a gidajen man MRS zuwa N739, yayin da kamfanin NNPCL ya rage farashin lita zuwa N815 a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Ana murna Dala ta karye, ƴan kasuwa sun sauke farashin gas din girki a Najeriya

Darajar Naira ta karu a kasuwar hada-hadar kudi ta gwamnati.
Wani mutumi zaune yana kirga dalolin Amurka da hoton Naira tare da Dala. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Naira ta lallasa Dala a kasuwar gwamnati

Bayanai daga Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa Naira ta shigo shekarar 2026 ne da ƙarfinta, inda a ranar Juma’a ta kai N1,430.84/$1, kuma ta ci gaba da ƙara daraja a kowace ranar kasuwanci, in ji rahoton Punch.

Rahoton ya nuna cewa Naira ta tashi zuwa N1,429.30/\$$ a ranar Litinin, sannan a ranar Talata, ta lula zuwa N1,419.06/$1, wanda ke wakiltar ƙaruwar kashi 0.72.

Ko da yake darakar kudin Najeriyar ta ƙaru da kashi 0.06 a ranar Laraba, amma Naira ta ci gaba da samun ci gaba har ta kai matsayin da ba a gani ba a sama da shekara guda.

Bambancin farashin Dala a kasuwar bayan fage

Tun daga farkon sabuwar shekarar, Naira ta yi ta ƙara daraja a kan Dala inda ta samu ƙaruwar kusan N17 tsakanin 31 ga Disambar 2025 zuwa 7 ga Janairun 2026.

Wannan nuna cewa kasuwar tana gudana ne cikin kwanciyar hankali ba tare da 'yan kasuwa sun firgita ba, ko don tunanin karancin Dala ko na musaya a kasuwar duniya.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya miliyan 141 za su fada cikin kangin talauci a 2026, an fadi dalili

Sai dai kuma, kasuwar bayan fage ta nuna akasin haka, inda Naira ta ɗan yi rauni da kashi 0.21 zuwa N1,467/$1 a lokacin da aka rufe hada-hada a ranar Laraba.

Gidajen man NNPCL da matatar Dangote sun sauke farashin fetur
Wani ma'aikaci ya na sayar da fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya sauke farashin fetur a MRS

Wannan nasara ta Naira na zuwa ne yayin da matatar man Dangote ta sanar da fara sayar da man fetur a faɗin ƙasa a kan N739 a kowace lita a gidajen man MRS, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.

Wannan ya faru sakamakon yarjejeniyar shekaru biyu ne na samar da ɗanyen mai tsakanin Dangote da NNPCL, wanda ya yi daidai da ƙudurin gwamnatin tarayya na samar da mai ga matatar da kuɗin Naira.

Idan za a iya tunawa, matatar ta taɓa dakatar da sayar da mai da Naira saboda ƙarewar kason ɗanyen mai, amma bayan sa bakin kwamitin gwamnati, an sake komawa sayar da man da Naira.

Kamfanin NNPCL ya sauke farashin fetur

Tun da fari, mun ruwaito cewa, NNPCL ya sanar da sake rage farashin litar man fetur da N20 a gidajen mansa, matakin da zai shafi masu saye da sayarwa.

Kara karanta wannan

Kananan yara 469 sun mutu a jihar Kano, bincike ya nuna abin da ya kashe su

Sabon farashin ya fara bayyana ne a wasu manyan gidajen mai a birnin tarayya Abuja, inda aka ce matakin ya biyo bayan wani umarni da aka ba kamfanin.

Duk da wannan ragin da aka samu, har yanzu farashin kamfanin NNPCL bai kai rangwamen na wasu gidajen mai da ke samun fetur daga matatar Dangote ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com