'Yan Najeriya Miliyan 141 Za Su Fada cikin Kangin Talauci a 2026, An Fadi Dalili

'Yan Najeriya Miliyan 141 Za Su Fada cikin Kangin Talauci a 2026, An Fadi Dalili

  • An yi hasashen cewa 'yan Najeriya miliyan 141 za su fada cikin talauci a wannan shekara ta 2026, wanda ke nufin kashi 62 na 'yan kasar
  • Rahoton PwC ya nuna cewa tsadar abinci da sufuri sune babban kalubalen da ke hana talakawa fita daga mawuyacin halin da suke ciki
  • Sai dai fadar shugaban kasa ta karyata wadannan alkaluma inda Sunday Dare ya yi bayani game da abubuwan da za a yi la'akari da su na zahiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani sabon rahoto mai ban tsoro da aka fitar ya nuna cewa kusan 'yan Najeriya miliyan 141 ne za su fada cikin kangin talauci a wannan shekarar.

Kamfanin binciken tattalin arziki na PwC ya fitar da rahoton, inda ya ce kashi 62 na al'ummar Najeriya, za su rasa arzikinsu, su fada talauci a 2026.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya fadi abin da ke shirin kora 'yan Kwankwasiyya zuwa jam'iyyar APC

Rahoto ya nuna cewa 'yan Najeriya miliyan 141 ne za su fada talauci a 2026.
Wasu mata na zaune a wani sansanin 'yan gudun hijira da aka ware masu a Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

Miliyoyin 'yan Najeriya za su fada talauci

Rahoton ya yi nuni da cewa duk da matakan da gwamnati ke ɗauka na gyara tattalin arziki, wasu manyan dalilai za su jefa miliyoyin mutane a talauci, in ji jaridar Daily Trust.

A cewar kamfanin PwC, hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin ƙaruwar kuɗaɗen shiga za su ci gaba da jefa iyalai da dama cikin mawuyacin hali kafin zaɓen 2027.

Rahoton ya bayyana cewa talakawa a Najeriya na kashe kusan kashi 70 na dukkan kuɗaɗen shigarsu wajen sayen abinci kaɗai, wanda hakan ke barinsu cikin mawuyacin hali idan farashi ya ƙara tashi.

Duk da akwai hasashen da ake yi na cewa hauhawar farashin kaya zai ragu nan gaba kadan, amma rahoton ya jaddada cewa tsadar makamashi, sufuri, da kuma faduwar darajar Naira za su ci gaba da sa farashin abinci da sauran muhimman buƙatu zama masu wahalar samu ga talakan Najeriya.

Kara karanta wannan

Kananan yara 469 sun mutu a jihar Kano, bincike ya nuna abin da ya kashe su

Bankin Duniya ya hango karuwar talauci

Bankin Duniya ma ya goyi bayan wannan hasashen, inda ya nuna cewa talauci a Najeriya zai kai kololuwa a wannan shekara ta 2026 kafin a samu raguwa kaɗan zuwa kashi 61 a shekarar 2027.

Wannan yana nuna babbar koma-baya ga tattalin arzikin ƙasar, idan aka yi la'akari da cewa a shekarar 2019, kashi 40 na ’yan Najeriya ne kawai ke zaune cikin talauci.

Sai dai kuma, fadar shugaban ƙasa ta nuna rashin amincewa da waɗannan alƙaluma, in ji rahoton Finance in Africa.

Fadar shugaban kasa ta karyata alkaluman da ke nuna cewa mutane miliyan 141 za su fantsama a talauci
Sunday Dare, mataimaki na musamman ga Shugaba Bola Tinubu, ya na aiki a ofishinsa. Hoto: @SundayDareSD
Source: Twitter

Martanin gwamnati kan alkaluman talauci

Sunday Dare, Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokan yaɗa labarai, ya bayyana cewa waɗannan ƙididdigo "ba su yi kama da zahirin abin da ke faruwa ba."

Hadimin shugaban kasar ya buƙaci masana su riƙa duba waɗannan alkaluma ta wata mahanga daban, yana mai cewa gwamnati na ƙoƙarin aiwatar da shirye-shiryen rage raɗaɗin talauci da bunkasa fannin noma domin rage tsadar rayuwa ga talakawa.

Kara karanta wannan

Wasu 'yan kasuwa sun hade da Dangote, za su kara sauke farashin fetur a Najeriya

Duk da haka, masana sun yi gargaɗi cewa ba tare da samar da ayyukan yi da inganta tsaro a gonaki ba, ƙoƙarin rage talauci zai kasance mai wahala a ƙasar.

Bankin Duniya ya ba Tinubu shawarwari

A wani labari, mun ruwaito cewa, Bankin Duniya ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da sauye-sauyen da za su kare talakawa daga hauhawar farashi.

Rahoton Bankin ya ce lamarin hauhawar farashi yana kara dagula rayuwar masu rauni, kuma babu wani ci gaba da za a iya samu a yaki da talauci.

Bankin Duniya ya ba da shawarwarin ne bayan ya fitar da alkaluma masu tayar da hankali, inda ya ce mutane sama da miliyan 42 za su fada cikin talauci a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com