Dangote Ya Aika Wasika ga ICPC, Ya Canza Shawara kan Korafin da Ya Shigar da Farouk Ahmed
- Alhaji Aliko Dangote ya janye korafin da ya shigar gaban hukumar ICPC kan tsohon shugaban hukumar kula da harkokin mai (NMDPRA)
- Lauyan Dangote ne ya tabbatar da janye korafin a wata wasika da ya aika wa ICPC mai dauke da kwanan watan 5 ga watan Janairu, 2025
- Tun farko rikici ya shiga tsakanin Dangote da Injiniya Farouk Ahmed ne kan zargin rashin gaskiya da taba dukiyar gwamnati da yake ofis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hamshakin attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote ya janye korafin da ya shigar gaban hukumar yaki da rashawa ta ICPC kan tsohon shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed.
Dr. O.J. Onoja (SAN), lauyan Dangote ya rubuta wa Hukumar ICPC wasika, inda ya sanar da ita cewa ya janye gaba ɗaya ƙorafin da aka shigar kan Injiniya Farouk Ahmed.

Source: Getty Images
Leadership ta rahoto cewa wasiƙar na ɗauke da kwanan wata 5 ga Janairu, 2025, da kuma taken “Sanarwar Janye Ƙorafi kan Injiniya Farouk Ahmed."
A wannan takarda, lauyan Dangote ya bayyana cewa a halin yanzu wani ɓangaren gwamnatin tarayya daban ne ke gudanar da binciken lamarin.
Dangote ya janye korafin da ya kai ICPC
Sai dai, mai magana da yawun ICPC, John Odey, ya ce duk da janye ƙorafin, hukumar za ta ci gaba da bincike, domin kare muradun jama’a da ƙasar Najeriya baki ɗaya.
A cewarsa:
“ICPC ta karɓi wasiƙar janye korafi mai kwanan wata 5 ga Janairu, 2025, wadda Dr. O.J. Onoja (SAN) da kamfaninsa, a matsayin lauyan Alhaji Aliko Dangote, suka miƙa wa hukumar.
“Wasiƙar ta bayyana cewa an janye ƙorafin da aka shigar ranar 16 ga Disamba, 2025, kan Injiniya Farouk Ahmed, tsohon shugaban NMDPRA, gaba ɗaya, tare da cewa wani jami’in tsaro na gwamnati ya karɓi binciken.”
Wane mataki hukumar ICPC za ta dauka?
Duk da haka, hukumar ICPC ta jaddada cewa, bisa tanadin sashe na 3(14) da 27(3) na dokar kafa ta, za ta ci gaba da bincike, domin kare muradun al’ummar Najeriya da ƙasar baki ɗaya.
“Hukumar ICPC za ta ci gaba da wannan bincike bisa doka, domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa, don amfanin Najeriya,” in ji Odey.

Source: Facebook
Tun farko dai Dangote ta shigar da korafin Farouk Ahmed gaban ICPC ne kan zargin biya wa yayansa kudin makaranta har Dala miliyan 5, wanda yake ganin ya fi karfin samunsa, kamar yadda Tribune ta kawo.
RAI ta shiga rikicin Dangote da Farouk
A wani rahoton, kun ji cewa Kungiyar RAI ta shigar da kara a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, tana neman a bincike game da rikicin Aliko Dangote da Farouk Ahmed.
A karar da RAI ta shigar, lauyan kungiyar Okere Nnamdi ya bukaci kotu ta ayyana cewa Farouk Ahmed ya aikata laifin karban kudi daga hannun wasu ba bisa ka'ida ba.
Kungiyar ta kuma bukaci kotu ta umarci Shugaba Tinubu da ya dakatar da Farouk Ahmed nan take, tare da tilasta wa hukumomin yaki da rashawa gudanar da bincike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


