Wata Sabuwa: Kotu Ta Kwace Kadarori 57 na Malami a Kano, Abuja da Wasu Jihohi 2
- Wata Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba da umarnin wucin gadi na kwace wasu kadarori da ake zargin na Abubakar Malami ne
- Mai shari'a Emeka Nwite ya ba da wa'adin kwanaki 14 ga duk wanda ke da hujjar mallakar dukiyoyin kafin kwace kadarorin gaba daya
- Wannan na zuwa ke bayan kotun ta ba da belin Malami da sauran wadanda ake tuhuma kan Naira biliyan 1.5 da sharudda masu tsauri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaka da tsohon Antoni Janar na Tarayya (AGF), Abubakar Malami, SAN.
Hukumar EFCC ce ta shigar da bukatar kwace kadarorin bisa zargin cewa Malami, tsohon ministan shari'a ya mallake su ta hanyar amfani da kudin haram.

Source: Facebook
Kotu ta amince da bukatar hukumar EFCC
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin a ranar Talata, yayin da yake yanke hukunci kan wata buƙatar gaggawa da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar, cewar The Nation.
Lauyan hukumar EFCC, Ekele Iheanacho (SAN) ne ya gabatar da bukatar a babbar kotun tarayya kuma ya samu nasarar amincewar mai shari’a Emeka Nwite.
Kwafin umarnin kotun da aka samu a ranar Laraba ya nuna cewa kadarorin da suka kunshi filaye da gine-ginen da abin ya shafa suna a Abuja, Kebbi, Kano da Kaduna.
Wannan na zuwa ne bayan kotun ta amince da bukatar belin Malami, 'dansa da kuma 'daya daga cikin matansa, wadanda EFCC ta gurfanar kan zarge-zargen sama da fadi da dukiyar kasa.
Kotu ta gindaya wa'adin makonni 2
A cikin hukuncin da kotun ta yanke game da batun kadarorin, Mai shari’a Nwite ya ce:
“Kotu ta bayar da umarnin wucin-gadi na ƙwace kadarorin da aka lissafo a jadawali na daya da ke ƙasa, waɗanda ake da hujjar cewa an same su ne ta haramtacciyar hanya."
Alkalin ya kuma umarci EFCC da ta wallafa umarnin ƙwace kadarori a jarida ta ƙasa, domin duk wanda ke da ta cewa lo ikirarin mallakar wadannan kadarorin ya gabatar da kansa cikin kwanaki 14.

Source: Twitter
Alkalin ya bada wa'adin kwanaki 14 ga duk wanda ke ganin hukuncin bai dace ba domin ya gabatar dalilin da ya sa ba za a ƙwace kadarorin gaba daya, a mallaka wa Gwamnatin Tarayya.
Daga bisani, alkalin ya ɗage shari’ar zuwa ranar 27 ga Janairu, domin EFCC ta ba kotu rahoto kan yadda ta bi umarnin wallafa hukuncin a jarida, kamar yadda Punch ta ruwaito.
An amince da bukatar belin Malami a kotu
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da beli ga tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami da matarsa da dansa.
Alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite, ya ce kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma zai bayar da Naira miliyan 500 a matsayin beli.
Kotun ta ce za su ci gaba da kasancewa a tsare har sai sun kammala cika dukkan sharudan belin da aka shimfida musu.
Asali: Legit.ng

