Karfin Hali: An Cafke Ɓarawo bayan Sace Motar Masarautar Bauchi
- Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta dakile yunkurin satar motar Toyota Hilux mallakar Majalisar Masarautar Bauchi
- Rahoton ya nuna cewa barawon ya sace motar ne a gidan mai na Inkiya yayin da direban ya tsaya sayen mai
- ‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargi a yankin Bayan Gari tare da kwato motar da ya yi yunkurin tserewa da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar cafke wani da ake zargin ya sace motar masarautar jihar Bauchi.
'Yan sanda sun dakile yunkurin satar motar kirar Toyota Hilux mallakar Majalisar Masarautar Bauchi a cikin birnin Bauchi.

Source: Facebook
An cafke barawon motar masarautar Bauchi
Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin Facebook a jiya Talata 6 ga watan Janairun shekarar 2025.
Lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, lokacin da Buhari Musa Umar, mamba a Majalisar Masarautar Bauchi, ya kai rahoton satar motar, cewar Leadership.
Buhari Musa ya sanar da tawagar sintirin ‘yan sanda da ke bakin shataletale kan hanyar Jos cewa an sace motar ne yayin da direba ya tsaya a gidan mai.
Rahoton ya ce an ajiye motar Toyota Hilux a gidan mai na Inkiya yayin da direban ya tsaya sayen fetur domin ci gaba da tafiya.
Direban ya bayyana cewa yana kan hanyar domin isar da sako ne zuwa karamar hukumar Ganjuwa domin kai aika daga Mai Martaba Sarkin Bauchi.
Ya ce bayan ya sauka domin shiga banɗaki na ɗan lokaci, wani mutum ya yi amfani da damar, ya tuka motar ya tsere.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, ya fitar ranar Talata 6 ga watan Janairun 2026, ya ce jami’ai sun dauki matakin gaggawa.
SP Habib ya bayyana cewa jami’an sun bi sawun wanda ake zargi tare da samun nasarar kwato motar a yankin Bayan Gari.
Ya kara da cewa an cafke wanda ake zargin a wurin tare da kwato motar Toyota Hilux da aka sace ba tare da wata matsala ba.

Source: Original
Alkawarin da 'yan sanda suka yi a Bauchi
Kakakin rundunar yan sanda ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin satar motar yayin da ake masa tambayoyi a ofishin ‘yan sanda.
SP Habib ya ce bincike na ci gaba, kuma ya tabbatar da cewa bayan kammala binciken za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.
Ya ce:
"Ana ci gaba da bincike wanda da zarar an kammala masa tambayoyi za a tura shi kotu."
A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kuma sanya jihar Bauchi ta kasance mai aminci ga kowa.
Bauchi: Matashi ya mutu a rikicin radin suna
Mun ba ku labarin cewa wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasu bayan rikici ya ɓarke a wajen bikin suna a Jihar Bauchi.
Rikicin ya samo asali ne daga sabani da ya shiga tsakanin wasu matasa da suka halarci taron raɗin sunan.
Da farko matashin ya suma bayan rikici ya yi zafi, kafin a garzaya da shi zuwa wurin kwararru inda aka ce ya rasu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


