Dasa Bam a Masallaci: An kuma Cafke Mutane 8, an Samu Muhimman Bayanai
- Sojojin Operation Hadin Kai suna ci gaba da cafke mutane bayan tashin bam a cikin masallaci a jihar Borno
- Rundunar ta kama karin mutane takwas da ake zargi da hannu a tayar da bam a wani masallacin Maiduguri
- Harin ya faru ne a watan Disamba 2025 a kasuwar Gamboru, inda bam ya kashe akalla mutane biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Sojojin Operation Hadin Kai sun kama wasu karin mutane takwas dangane da harin kunar bakin wake da ya afku a masallaci a Maiduguri, Borno.
Hakan ya zo ne kwanaki uku bayan kama wanda ake zargin shi ne jagoran harin, Sheriff Umar, da dakarun suka yi a babban birnin jihar Borno.

Source: Original
Harin ya faru a ranar 24 ga Disamba 2025, lokacin da dan kunar bakin wake ya tayar da bam a masallacin kasuwar Gamboru a Maiduguri da ke jihar Borno, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Borno: Sojoji sun taka bama bamai a hanyar kai wa ƴan ta'adda farmaki, an yi asarar rayuka
Yadda dasa bama-bamai ya zama kasuwanci a Arewa
Hakan ya biyo bayan cafke wani matashi a jihar Yobe wanda ake zargin yana daga cikin masu dasa bama-bamai wanda ke ajalin mutane da dama.
Dakarun Operation Hadin Kai sun cafke wani da ake zargin ɗan kunar bakin wake na Boko Haram ne a Najeriya.
Wanda ake zargin Ibrahim Mohammed ya bayyana yadda aka shirya harin masallacin kasuwar Gamboru da ya kashe mutane biyar tare da jikkata 32.
Ya ce bayan fashewar bam din, ya koma wurin yana taimakawa, yana ɗaukar gawarwaki zuwa cikin motoci domin ba su kulawa da ta dace a lokacin.
Fashewar bam din ta kashe akalla mutane biyar, tare da barin wasu 35 da raunuka daban-daban wanda ya tayar da hankulan al'umma baki daya.
Harin bam: Abubuwan da sojoji suka gano
Jami’in yada labarai na Operation Hadin Kai, Sani Uba, ya ce an kama su ne a Yan Lemu, Mubi ta Kudu da ke jihar Adamawa, yayin wani aiki.
Ya ce bincike a gidan su ya gano kudi, wayoyin hannu, takardun shaida, katunan ATM, kayan ado, inda ya ce ana ci gaba da bincike yanzu.
Uba ya kara da cewa wani da ke tsare ya gano manyan mutane biyu a matsayin masu samar da kayan hada bam din harin, cewar rahoton Arise TV.
Ya ce an danganta wasu mazauna gidan da cibiyar, yayin da bincike ke ci gaba domin bankado dukkan hanyoyin sadarwa na kungiyar.
Sojoji sun taka bama-bamai a Borno
Mun ba ku labarin cewa sojojin Najeriya sun gamu da tsautsayi bayan taka wadansu bama-bamai a hanyar Maiduguri–Gubio a jihar Borno.
Sojojin na kan hanyarsu zuwa wani aiki a dajin Sasawa da ke makwabciyar jihar Yobe don fatattakar yan ta'adda lokacin da lamarin ya faru wanda ya tayar da hankula.
Rahotanni sun nuna ’yan Boko Haram ne suka dasa bam din da daddare, kuma ya yi sanadin asarar rayukan sojoji wanda hakan ya sake jefa fargaba a zukatan al'umma kan yaki da ta'addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
