Makiyaya Dauke da Makamai Sun Mamaye Garuruwa 2 a Benue, Mutane Sun Shiga Fargaba

Makiyaya Dauke da Makamai Sun Mamaye Garuruwa 2 a Benue, Mutane Sun Shiga Fargaba

  • Bakin makiyaya dauke da makamai sun mamaye wasu yankunan jihar Benue, lamarin da ya jefa mutane a cikin tashin hankali
  • Shugabannin al'umma sun yi kira ga gwamnati da ta tura jami'an tsaro cikin gaggawa a wadannan yankunan don kare rayukan jama'a
  • Mazauna wadannan yankuna sun bayyana yadda suka tsorota biyo bayan wassu hare-hare da ake zargin yan ta'addan ne suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Mazauna wasu sassan jihar Benue sun shiga halin fargaba yayin da aka samu rahoton bullar wasu bakin mutane da ake zargin makiyaya ne.

Hankulan mutane sun tashi ne da aka ga makiyayan dauke da makamai tare da kuma dubban shanu a kananan hukumomin Logo da Gwer ta Yamma.

Fulani Makiyaya a garuruwan Benue
Wani jami'in tsaro a bakin aiki da wani makiyaya yana kiwon shanu a cikin gona. Hoto: GettyImages
Source: Getty Images

Makiyaya dauke da makamai sun bulla Benue

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe wani uban daba a Kano da rikici ya barke tsakanin kungiyoyi 2

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa an fara ganin motsin makiyayan ne tun kafin ranar 25 ga watan Disamba, 2025, amma yanzu da aka shiga 2026 lamarin ya kara munana.

Wasu daga cikin mazauna wadannan yankuna sun bayyana cewa sun ga makiyayan suna tsallakawa zuwa mazabar Tombo daga kananan hukumomin Awe da Keana dake makotaka da jihar Nasarawa.

Majiyoyi daga yankin Logo sun bayyana cewa wadannan mutane sun mamaye garuruwa daban daban, kamar dai yadda aka ga sun kafa sansani a bayan garin Gidin-Mangor.

Hakazalika, wasu majiyoyi sun ce, an ga makiyayan sun samu mafaka a rugagen Fulani da kauyukan da mutane suka gudu suka bari saboda hare-haren 'yan bindiga.

Majiyoyi sun bayyana cewa ganin makiyayan ya tilasta wa mutane takaita zirga-zirga tare da dagula harkokin kasuwanci a yankunan Mbaiwen da Mbazar.

Mazauna Benue sun nemi daukin gaggawa

Wani babban abin damuwa ga mazauna yankin shi ne rade-radin cewa wadannan mutane na iya kasancewa yan ta'adda ne dake gujewa hare-haren dakarun Amurka ko na sojin Najeriya daga wasu jihohin.

Shugabannin al'umma sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta tura karin jami'ai zuwa mazabar Tombo, wadda ke da iyaka da jihohin Nasarawa da Taraba, hanyoyin da bata-gari kan bi don aikata barna.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga, an ceto mutanen da aka sace a Zamfara

Sun jaddada cewa bukatar matakin gaggawa ya zama dole kafin lamarin ya kazance, kamar yadda wani rahoto na jaridar Daily Post ya nuna.

Mazauna jihar Benue sun nemi daukin jami'an tsaro da aka samu bullar makiyaya dauke da makamai
Taswirar jihar Benue, inda aka samu bullar makiyaya dauke da makamai. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mutanen Benue na fargabar harin 'yan bindiga

Haka zalika, a yankin Tse Ati dake mazabar Mbabuande a karamar hukumar Gwer ta Yamma, an bayar da rahoton ganin makiyaya dauke da makamai a ranar Litinin, wanda hakan ya sanya mazauna garin cikin zullumi.

Kodayake ba a kai hari ba tukuna, shugabannin yankin sun bayyana cewa alamun da suke gani ba su da kyau, don haka suke neman agajin jami'an tsaro.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda na jihar Benue, DSP Udeme Edet ba.

Mutane sun fara tserewa daga gidajensu

A wani labari, mun ruwaito cewa, mutane sun fara tserewa daga gidajensu a wasu garuruwan Neja saboda tsoron hare-haren 'yan bindiga.

'Yan ta'adda sun yi barazanar dawowa yankin bayan sun kashe mutane fiye da 40 tare da kona coci da ofishin yan sanda da kasuwa.

Shugabannin addini da mazauna yankin sun koka kan janyewar sojoji daga yankin, wanda hakan ya bar talakawa cikin hatsari da fargaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com