Kano: Wasu Yara Sun Fadi Dalilin Murna da Rasuwar Mahaifinsu bayan Shekaru 20
- Masu hakar masai sun gano gawar wani mutum bayan fiye da shekaru 20 da birne shi a Unguwar Tudun Yola, jihar Kano
- Iyalan mamacin sun nuna farin ciki tare da ɗaukar lamarin a matsayin rahamar Allah bayan ganin gawar kamar yau ta shiga kabari
- Sai dai Malamin addinin Musulunci ya ya tabbatar da sake wa mamacin wuri, amma ya fadi kuskure daya da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu yara a Unguwar Tudun Yola da ke Jihar Kano sun bayyana farin cikinsu bayan gano gawar mahaifinsu, wadda aka tono yayin da ake aikin haka masai.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ma’aikata da ke aikin tonon rami sun ci karo da gawar, inda nan take suka kira wanda ya ba su aikin.

Source: Original
A labarin da aka wallafa a shafin Facebook na Freedom Radio Nigeria, an bayyana cewa gawar ta kasance lafiya kalau, ba tare da ta lalace ba.
An gano gawar sama da shekaru 20 a Kano
Rahoton da fitaccen ɗan jarida Nasiru Salisu Zango ya kawo ya nuna cewa bayan kiran wanda ya ba da aikin ne aka dakatar da aikin hakar masan.
Iyalan mamacin sun bayyana farin cikinsu, inda suka ɗauki lamarin a matsayin wata alama da ke nuna cewa mahaifinsu ya samu rahamar Allah SWT.
A cewar iyalin mamacin:
“Suna yi min aiki, sai suka kira ni a waya, suka ce sun fasa wata tukunya amma sun ga likkafani a ciki. Sai na ce su rufe su bar aikin, zan zo na gani.”
“To da na zo na gani, dama sun rufe da dutse haka. Da na buɗe na gani, na tabbatar da cewa mutum ne a ciki. Gaskiya Alhamdulillah na ji daɗi, saboda dukkan mamaci abin da yake fata shi ne kyakkyawan ƙarshe.”
“Kuma duk mutumin da aka samu adadin shekara 20, aka zo a tono gawarsa amma babu abin da ya same shi, to za ka ji daɗi a ranka.”
’Yan uwan mamacin, waɗanda ba a bayyana sunayensu ba, sun kuma bayyana fatan Allah SWT Ya ƙara masa rahama har zuwa ranar kiyama.
An sake yi wa mamacin sallah a Kano
Rahoton ya ƙara da cewa bayan gano gawar tana lafiya kalau, sai aka sake yi mata sallar jana’iza, sannan aka sauya mata wuri.
Da aka tuntubi fitaccen malamin addinin Musulunci kuma shugaban zauren malamai na Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa babu laifi don a sake wa mamacin makwanci.

Source: Facebook
Sai dai ya ce babu wani dalili a Musulunci da ya nuna cewa ana sake yi wa gawa sallah bayan an riga an yi mata sutura kuma an birne ta.
A kalaman Shehin malamin:
“Wannan aiki ne mai kyau domin ya afku a zamanin sahabbai a lokacin Mu’awiyya yana Amirul Mu’uminin, amma sake sallar da suka yi babu dalili. Ra’ayin kansu ne kawai, ba bisa ilimi ba, domin babu hujjar sake yi wa gawa sallah.”
Ya ƙara da cewa Musulunci ya halatta tono gawa domin sauya mata wuri idan akwai buƙatar amfani da wurin.
Sheikh Ibrahim Khalil ya kara da cewa jahilci ne ke sa wasu mutane su rika cece-kuce idan irin wannan lamari ya faru.
Kano: Yara sun kai karar mahaifnsu a kotu
A baya, mun wallafa cewa fitaccen attajiri kuma dattijo a Jihar Kano, Alhaji Isma’ila Mai Biskit, ya shiga wani hali na damuwa da ƙunci sakamakon rikici da ya ɓarke a cikin iyalinsa.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ’ya’yan Alhaji Isma’ila Mai Biskit ne suka kai shi gaban kotu, inda suke zargin cewa mahaifinsu ba ya kamu da ciwon mantau.
A cewarsa Alhaji Mai Biskit, wannan al'amari ya ba shi mamaki, ganin cewa yaran ba su hawa ko sauka a fafutukar da ya yi wajen tara dukiyarsa tun yana matashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


