Nentawe: Shugaban APC Ya Kausasa Harshe kan Hare Haren 'Yan Ta'adda a Neja

Nentawe: Shugaban APC Ya Kausasa Harshe kan Hare Haren 'Yan Ta'adda a Neja

  • 'Yan ta'adda sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba yayin wasu hare-hare da suka kai a jihar Neja
  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi Allah da kashe-kashen da 'yan ta'addan suka yi
  • Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa wadannan ayyukan na rashin imani ba abu ba ne wanda za a yarda da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi kakkausar suka kan hare-haren ta’addanci da aka kai a wasu kauyuka da ke kananan hukumomin Agwara da Borgu a jihar Neja.

Rahotanni sun ce hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar akalla ’yan Najeriya 60 tare da sace mutane da dama, ciki har da mata da ƙananan yara.

Nentawe ya yi Allah wadai da hare-haren 'yan ta'adda a Neja
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai sa shi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Abimbola Tooki, ya fitar a ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake ta'addanci a Neja awanni bayan kashe mutane

Me Shugaban APC ya ce kan hare-haren 'yan ta'adda?

Yilwatda ya bayyana hare-haren a matsayin dabbanci, rashin imani, kuma abin kyama da ba za a taɓa amincewa da shi ba, amma ya nuna kwarin gwiwa cewa Najeriya za ta yi nasara a karshe.

Ya bayyana matukar damuwarsa kan rahotannin ci gaba da tashin hankali a yankunan da abin ya shafa, ciki har da kisan manoma da talakawa a Kasuwan Daji da Kaima, kone kasuwanni, lalata gidaje da wuraren ibada, da kuma sace ɗalibai daga makarantar Papiri.

Nentawe ya yi ta'aziyya ga Gwamna Bago

Shugaban na APC ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, gwamnatin jihar, da kuma iyalan waɗanda abin ya shafa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da hakan.

Ya tabbatar musu da cewa jam’iyyar APC tana tare da su gaba ɗaya a wannan lokaci na jimami da bakin ciki.

“Wannan tashin hankalin da ake yi wa ’yan kasa marasa laifi cin mutunci ne a gare mu. APC na tsaye daram tare da al’ummar jihar Neja, kuma muna tabbatar musu da cewa za mu ba su goyon baya."

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan bukatar neman belin kwamishinan Bauchi

Farfesa Nentawe Yilwatda

Shugaba Tinubu ya samu yabo

Ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan gaggawa da ya ɗauka, ciki har da umarnin da ya bai wa manyan jami’an tsaro na farautar masu laifin tare da ceto duk waɗanda aka sace.

Shugaban APC ya soki harin 'yan ta'adda a Neja
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taro Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Yilwatda ya ce bayanan sirri na tsaro sun nuna cewa maharan ’yan ta’adda ne da ke tserewa daga jihohin Sokoto da Zamfara, yana mai kara da cewa tsarin tsaron Najeriya yana cikin shirin ko-ta-kwana.

Ya kuma sake jaddada cikakken goyon bayan APC ga kudurin gwamnati na kawo ƙarshen ta’addanci, tare da kira ga ’yan ƙasa da su ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro, yana mai tabbatar da cewa Najeriya za ta yi nasara a karshe, Insha Allah.

'Yan ta'adda sun farmaki 'yan sanda

A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun farmaki wani shingen binciken 'yan sanda a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Matakin da gwamnati ta ɗauka bayan ƴan ta'adda sun kashe fiye da mutum 30 a Neja

'Yan ta'addan sun kona shingen binciken na 'yan sanda wanda yake a karamar hukumar Borgu mai fama da rashin tsaro.

Hakazalika, 'yan ta'adda sun kona kayan amfanin gona na manoma tare da kwashe wasu kayayyakin zuwa cikin daji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng