Masanin Tsaro Ya Faɗi Yadda Gwamnati Ta Yi Sakaci aka Kashe Mutane 40 a Neja

Masanin Tsaro Ya Faɗi Yadda Gwamnati Ta Yi Sakaci aka Kashe Mutane 40 a Neja

  • Fitaccen masanin tsaro, Dr. Suleiman Isyaku Mohammad, ya nuna takaici kan kisan jama’a a Jihar Neja
  • Dr. Suleiman Isyaku Mohammad, ya zargi gwamnati da sakaci da gaza daukar matakan kariya tun da wuri
  • Ya bayyana cewa tun bayan harin Papiri inda aka sace dalibai ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan tsaron jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Fitaccen masanin tsaro a Najeriya, Dr. Suleiman Isyaku Mohammad, ya bayyana matuƙar takaici da damuwa kan yadda ƴan ta’adda suka samu damar kwashe awanni suna kashe mazauna Jihar Neja.

A wata hira da ya yi da Legit, Dr. Suleiman Isyaku Mohammad ya ce abin takaici ne yadda gwamnati ta yi sakaci da al’amuran tsaro a muhimman matakai, musamman a matakin al’umma.

Kara karanta wannan

Matakin da gwamnati ta ɗauka bayan ƴan ta'adda sun kashe fiye da mutum 30 a Neja

Masanin tsaro ya yi tir da harin Neja
Wani sashe na kauyen da yan ta'adda suka kai wa hari a Naje Hoto: @MP_Muye
Source: Twitter

Jaridar Punch ya bayyana cewa wasu mahara sun kai mummunan hari a karamar hukumar Borgu da ke Jihar Neja, inda aka kashe mutane sama da 40, lamarin da ya jefa yankin cikin firgici da jimami.

Masanin tsaro ya soki gwamnati kan harin Neja

Masanin tsaro, Dr. Suleiman Isyaku Mohammad, ya ce irin wannan mummunan hari na tilasta al’umma su rika tambayar inda kudin tsaro da ake warewa jihohi da hukumomi ke tafiya.

A cewarsa:

“Ana rayuwa amma babu wani tsari ko mizani da ke nuna ana duba tsaro yadda ya kamata. Babu shi, ballantana a ce idan an ga wata alama za a bibiya domin a gano abin da ke faruwa. A maimakon haka, sai dai a dogara da rahoto bayan wani ya yi waya ko ya sanar.”
“Bangaren Jihar Neja, ai ba yanzu aka fara samun irin wadannan hare-hare ba, amma wannan ya fi kowanne muni. Duk shekara ana ware kudin tsaro, ana yin kasafi kan ‘yan sanda da sauran hukumomi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni bayan 'yan ta'adda sun yi ta'addanci a Neja

"Haka kuma, muna da DSS da ya kamata su rika bayar da rahotannin sirri.”

Masanin tsaron ya ce akwai labarin cewa bayan cire tallafin mai, jihohi sun kara samun kuɗi daga asusun tarayya, inda ya yi mamakin abin da ake yi da kuɗin.

Gwamnati ta samu shawarar kwararre a harkar tsaro

Dr. Suleiman Isyaku Mohammad ya jaddada bukatar gwamnati ta sauya salon tafiyar da tsaro, ta fara daukar matakan kariya tun kafin faruwar hari, ba wai ihu bayan an riga an kashe jama’a ba.

Masanin tsaro ya dora alhakin nasarar harin Neja a kan gwamnati Hoto: Niger State
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago Hoto: Niger State
Source: Facebook

Ya ce:

“Duk abin da zai faru, musamman wanda ya shafi tsaro, dole ne ya fara nuna alama. Aikin jami’in tsaro shi ne neman wannan alama, ba jiran laifi ya auku ba.”

Ya bayyana cewa rashin jami’an tsaro, karancin kayan aiki na zamani, ko rashin duk wata alamar gwamnati a wani yanki, duk suna daga cikin manyan barazana ga rayuwar al’umma.

Masanin ya nanata cewa lokaci ya wuce na jiran ƴan ta’adda su kashe jama’a sannan a juya lamarin zuwa batun siyasa.

Kara karanta wannan

Mamdani: Musulmin da ya ci zabe ya ruguza shirin Isra'ila a Amurka

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su daina caca da rayukan mutanen da suka zabe su, domin akwai damar kare afkuwar harin Neja.

Dr. Suleiman Isyaku Mohammad ya kara da cewa tun a lokacin da aka kwashe dalibai sama da 100 a Papiri ya kamata a mayar da hankali kan tsaron yankin.

Ya kuma gargadi cewa idan jama’a suka fara daukar tsaro a hannunsu, hakan na iya haifar da babbar ɓarna da rikici a kasa.

Mutane na barin gidajensu a Neja

A baya, mun ruwaito cewa mazauna yankunan karkara na ƙananan hukumomin Agwara da Borgu a Jihar Neja na cikin fargaba da tashin hankali, sakamakon barazanar da ’yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa jama’a da dama sun fara barin gidajensu, suna tserewa zuwa garuruwa ko yankuna da suke ganin sun fi samun tsaro saboda tsoron dawowar miyagun.

Matakin ya biyo bayan sakonnin barazana da alamun shirin kai sabon hari da mazauna yankunan ke cewa suna karɓa daga ’yan bindiga bayan harin Borgu da ya kashe sama da mutum 40.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng