Borno: Sojoji Sun Taka Bama Bamai a Hanyar Kai wa Ƴan Ta'adda Farmaki, An Yi Asarar Rayuka
- Sojojin Najeriya sun Najeriya sun gamu da tsautsayi bayan taka wadansu bama-bamai a hanyar Maiduguri–Gubio a jihar Borno
- Sojojin na kan hanyarsu zuwa wani aiki a dajin Sasawa da ke makwabciyar jihar Yobe don fatattakar yan ta'adda
- Rahotanni sun nuna ’yan Boko Haram ne suka dasa bam din da daddare, kuma ya yi sanadin asarar rayukan sojoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Borno – An tabbatar da mutuwar sojojin Najeriya tara bayan wani bam da aka kera da hannu (IED) ya tashi a kan hanyar Maiduguri zuwa Gubio, a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a daren Lahadi, inda jami’an soji da na rundunar hadin gwiwar fararen hula (CJTF) suka tabbatar da aukuwar harin da mutuwar zaratan dakarun.

Source: Facebook
BBC Hausa ta wallafa cewa majiyoyi daga bangaren tsaro sun shaida cewa sojojin na tafiya ne daga Maiduguri ta garin Gubio domin kai farmaki a dajin Sasawa da ke cikin jihar Yobe.
Bam ya tashi da sojoji a Borno
The Guardian ta wallafa cewa sojojin na cikin tafiya ne a lokacin da bam din ya tashi kusa da Gubio, hedikwatar karamar hukumar Gubio a jihar Borno.
Bincike ya nuna cewa ’yan kungiyar Boko Haram ne suka dasa bam din a gefen hanya da daddare, suna jiran wucewar ayarin sojoji.
Rahoton ya ce sojojin sun ratsa hanyar a ranar Asabar, inda suka tsaya a wani sansanin soji da ke bakin hanya, kafin su ci gaba da tafiyarsu washegari.
Wata majiya ta ce:
“Sojojin sun tsaya a sansanin soji da ke bakin hanya a ranar Asabar, sannan suka shirya ci gaba da tafiya a ranar Lahadi. A yayin tafiyar ne bam din da aka dasa a hanya ya tashi.”

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni bayan 'yan ta'adda sun yi ta'addanci a Neja
Wani babban jami’in soja ya tabbatar da cewa baya ga mutuwar sojojin tara, wasu da dama sun jikkata, inda wasu suka samu raunuka a hannaye, kafafu da kuma kai.
Borno: Sojoji sun rasu, wasu sun jikkata
Rahotanni sun nuna cewa sojojin da lamarin ya shafa na cikin Bataliya ta 145 da ke Damasak, karkashin Birgediya ta 5 ta sojojin Najeriya, wadda hedikwatarta ke Maimalari Cantonment a Maiduguri.
Majiyoyi sun jaddada cewa harin ba kwanton bauna ba ne, illa bam din da aka dasa a hanya tun kafin wucewar sojoji.

Source: Original
Rahoton ya ce wannan na daga cikin dabarun da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen kai hari kan jami’an tsaro a Borno da kewayenta.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.
A ’yan shekarun nan, kungiyoyin Boko Haram da ISWAP na ci gaba da kai hare-hare ta hanyar amfani da motoci dauke da makamai da kuma bama-bamai a manyan hanyoyi da ke kusa da dajin Sambisa da tafkin Chadi.
Sojoji sun kutsa dajin Sambisa
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Hadin Kai ta kai wani gagarumin farmaki a cikin Dajin Sambisa da ke jihar Borno, inda ta yi artabu da ’yan Boko Haram.
Rahotanni sun nuna cewa an hallaka wasu daga cikin ’yan ta’addan yayin da sauran suka tsere domin tsira da rayukansu, wanda ya nuna gagarumin nasara da dakarun suka samu.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an gudanar da samamen ne a ranar 29 ga Disamban 2025, bayan samun sahihin bayanan sirri kan motsin ’yan ta’adda a wasu sassan dajin Sambisa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

