'Yan Ta'adda Sun Sake Ta'addanci a Neja Awanni bayan Kashe Mutane
- 'Yan ta'adda dauke da makamai sun kara kai hari a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
- Tsagerun 'yan ta'addan sun kai harin ne kan wani shingen binciken 'yan sanda da ke kan iyaka a karamar hukumar Borgu
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da bayyana cewa ta tura karin jami'an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari kan wani shingen bincike na rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Neja.
'Yan ta'addan sun kai harin ne a kauyen New Kalli da ke karamar hukumar Borgu a jihar Neja.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa harin ya faru ne da misalin tsakar dare a ranar Lahadi, 4 ga watan Janairun 2026.
Harin na zuwa kasa da awanni 48 bayan da aka kashe ‘yan kasuwa da manoma da dama a Kasuwar Daji, wadda ke a cikin karamar hukumar Borgu.
'Yan ta'adda sun farmaki 'yan sandan Neja
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun cinna wa dakin da ake amfani da shi a matsayin shingen ‘yan sandan kan iyaka wuta, lamarin da ya janyo lalacewar kayayyakin jami’an tsaron.
Haka kuma, 'yan ta'addan sun kone amfanin gona na manoma a yankin.
Ko da yake ba a samu asarar rai ba, amma lamarin ya kara tsoratarwa da razanar da manoma da sauran mazauna yankin.
Wata majiya ta ce maharan sun zo ne a kan babura, inda suka kone masaukin jami’an tsaro, suka lalata amfanin gona, tare da kwashe wasu kayayyakin kansu kafin su tsere.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in kula da bala’o’i na karamar hukumar Borgu, Musa Saidu, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da tantance barnar da aka yi.
Me 'yan sanda suka ce kan harin?
Haka zalika, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar harin.

Source: Original
“A ranar 4 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 10:30 na dare, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan shingen sintiri na ‘yan sandan kan iyaka da ke kauyen Kale, ta hanyar Borgu."
"Jami’an ‘yan sanda sun yi musayar wuta mai tsanani da su, inda suka fatattaki maharan. Sai dai kuma shingen tsaron ya kama da wuta a yayin artabun. Daga baya an dawo da zaman lafiya, kuma an tura karin jami’an tsaro yankin."
- SP Wasiu Abiodun
'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makami sun kai hari kan shingen bincike na jami'an tsaron hukumar NSCDC a jihar Neja.
Hukumar NSCDC ta tabbatar da cewa 'yan bindigan sun kai harin ne kan shingen binciken jami’anta a kan titin Wawa-Babanla na karamar hukumar Borgu
Maharan wadanda suka zo da yawa, sun kai harin ne da tsakar dare, sai dai ba su samu damar yin barna ba saboda kokarin jami’an da ke bakin aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

