'Mutane Sun Fara Guduwa,' Halin da Ake ciki a Neja bayan Kashe fiye da Mutum 40
- Daruruwan mutane sun fara tserewa daga gidajensu a wasu garuruwan jihar Neja saboda tsoron sake fuskantar hare-haren 'yan bindiga
- 'Yan ta'adda sun yi barazanar dawowa yankin bayan sun kashe mutane fiye da 40 tare da kona coci da ofishin yan sanda da kasuwa
- Shugabannin addini da mazauna yankin sun koka kan janyewar sojoji daga yankin, wanda hakan ya bar talakawa cikin hatsari da fargaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - A halin da ake ciki mazauna yankunan karkara na ƙananan hukumomin Agwara da Borgu a jihar Niger na cikin tashin hankali da zaman dari-dari.
Mazauna waɗannan yankuna sun fara tserewa daga gidajensu zuwa garuruwa mafi tsaro, sakamakon barazanar da ’yan bindiga suka yi na cewa za su dawo domin ci gaba da kisan gilla.

Source: Original
Zargin janyewar sojoji a Neja
Wannan fargaba ta ƙaru ne biyo bayan harin ranar Asabar, 3 ga watan Janairu, 2026, inda aka kashe mutane 42 bayan an ɗaure su, sannan aka yi garkuwa da mata da yara da dama, in ji rahoton Punch.
Wani abin damuwa da mazauna garin suka bayyana shi ne zargin cewa dakarun sojin da aka tura yankin jim kaɗan bayan harin, sun janye daga wurin, wanda hakan ya bar talakawa ba tare da wani tsaro ba.
Mazauna ƙauyukan Kwana, Tugan Salama, da Papiri sun koka da cewa babu jami’an tsaro a kusa da su, alhali suna samun saƙonni da alamun cewa ’yan bindigar suna shirin sake kawo masu hare-hare.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ’yan bindigar sun ma ba da lambar waya ga wasu mutane don a kai wa shugabannin yankin, a matsayin nuna ƙarfin ikonsu.
Ta hanyar da 'yan bindiga suka kai hari Neja
Darekta a fannin sadarwa na cocin darikar Katolika ta Kontagora, Rev. Father Matthew Kabirat, ya bayyana cewa halin da ake ciki yanzu ya zama abin ban tsoro.
Ya ce tun daga ranar 28 ga Disamba, 2025, ’yan bindiga kusan 60 a kan babura suka mamaye yankin, inda suka rinka kai hare-hare, suna cin karensu ba babbaka.
Rahoto ya nuna cewa 'yan ta'addar sun shiga yankin Agwara da Borgu ne ta gandun dabbobi na Borgu zuwa jihar Kebbi, inda suka kashe mutane a ƙauyen Kaiwa da Gebe, kafin su dawo jihar Niger su ƙona ofisoshin ’yan sanda da lalata kayayyakin coci a Sokonbora.
An sake sace wasu daliban Papiri
Mafi ban tausayi a cikin wannan yanayi shi ne halin da ɗaliban makarantar Papiri suke ciki, inda ake fargabar an sake sace wasu daga cikinsu, a cewar rahoton Premium Times.
Waɗannan dai su ne daliban da aka ceto su kwanan baya daga hannun masu garkuwa, amma yanzu sun sake komawa 'yar gidan jiya.
Wani magidanci mai suna Abuka ya bayyana cewa ɗiyarsa, wadda tana ɗaya daga cikin waɗanda aka sako a baya, tana cikin wani mummunan yanayi na firgici wanda zai iya shafar rayuwarta na dindindin.

Source: Facebook
An roki gwamnati ta kafa sansanin tsaro
Al’ummar yankin sun yi kira na gaggawa ga gwamnatin tarayya da ta kafa runduna ta musamman wadda za ta samu matsuguni na dindindin a kusa da dajin Borgu.
Sun jaddada cewa muddin ba a lalata maɓoyar ’yan bindigar da ke cikin dajin Kainji ba, to garuruwan yankin za su ci gaba da rayuwa ne a cikin rashin zaman lafiya.
Jihar Niger na ci gaba da fuskantar ƙalubale daga ’yan bindigar da ke amfani da manyan dazuzzuka a matsayin mafakarsu yayin kai hare-hare cikin garuruwa.
Gwamnan Neja ya magantu kan harin Borgu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Mohammed Umaru Bago, ya yi tir da kakkausan harshe game da harin ta’addancin da aka kai wa mazauna ƙaramar hukumar Borgu.
Gwamna Bago, ta bakin babban sakataren yaɗa labaransa, Bologi Ibrahim, ya bayyana harin da aka kai Kasuwan Daji da ke yankin Demo a matsayin danyen aiki na rashin imani.
Gwamna Bago ya tabbatar da cewa dakarun tsaro na haɗin gwiwa suna bin sawun 'yan ta'addan domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


