Kotu Ta Yi Hukunci kan Bukatar Neman Belin Kwamishinan Bauchi
- Hukumar EFCC ta fara shari'a a gaban kotu da kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu kan zargin daukar nauyin ta'addanci
- Bayan fara shari'a, Yakubu Adamu, ya mika bukatarsa a gaban kotun da ke Abuja kan a bayar da belinsa
- Sai dai, yayin zaman kotun na ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2026, Mai shari'a Emeka Nwite ya yanke hukunci kan bukatar da kwamishinan ya gabatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan bukatar neman beli da kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, ya shigar a gabanta.
Babbar kotun ta ki amincewa da ba da beli ga Yakubu Adamu, wanda ke fuskantar shari’a kan zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci da kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 9.7.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa alkalin kotun, mai shari'a Emeke Nwite ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2026.
Kotu ta ki ba da belin kwamishinan Bauchi
Kotun ta kuma ki amincewa da bukatar beli ga sauran mutane uku da ake shari’ar tare da su, jaridar The Punch ta dauko labarin.
Mai shari'a Emeka Nwite, wanda ke jagorantar shari’ar, ya ce laifuffukan da ake zargin waɗanda ake tuhuma da su na barazana ga tsaron kasa da lafiyar al’umma.
Ya bayyana cewa laifuffukan da suka shafi ta’addanci na lalata tsarin zaman lafiya da tsaron jama’a.
Hakazalika ya ce sakin waɗanda ake tuhuma kafin kammala shari’a na iya jefa al’umma cikin haɗari, wanda hakan shi ne dalilin da ya sa kotu ta ƙi bayar da belin.
Sai dai kuma, alkalin kotun ya umarci a gaggauta sauraron shari’ar.
“Ba na mantawa da tanadin kundin tsarin mulki na sashe na 36(5) wanda ya tanadi cewa duk wanda ake tuhuma da laifi ana ɗaukarsa a matsayin mara laifi har sai an tabbatar da laifinsa.”

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni bayan 'yan ta'adda sun yi ta'addanci a Neja
“Amma dole ne na bayyana cewa wannan tanadi ba cikakke ba ne. A yayin la’akari da neman beli, dole ne a duba dukkan muhimman dalilai.”
- Emeka Nwite
Laifuffukan da ake tuhumarsu na da girma
Mai shari’ar ya kara da cewa ya duba takardun hujjojin da ke gaban kotu, ciki har da bayanan Dan Lawan Abdulmumuni da sauran shaidu na ɓangaren gwamnati.
“Na kuma lura cewa laifuffukan da suka shafi ta’addanci na barazana ga tsarin zaman lafiya, kuma sakin waɗanda ake tuhuma kafin shari’a na iya jefa jama’a cikin haɗari."
- Emeka Nwite

Source: Twitter
Ya ce a ra’ayinsa, ɓangaren gwamnati ya samu nasarar gabatar da hujjoji da ke nuna yiwuwar alhakin aikata laifi a kan Yakubu Adamu da sauran waɗanda ake tuhuma.
“Saboda haka, a gani na, adalci zai fi tabbata idan aka gaggauta sauraron wannan shari’a."
- Emeka Nwite
EFCC ta tabo batun shari'ar Yahaya Bello
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa, ta yi magana kan shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da shari'ar tsohon gwamnan a gaban kotu kan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
EFCC ta bayyana cewa ba a samu Yahaya Bello da laifi ba har sai kotu mai cikakken iko ta tabbatar da hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

