Zargin Nuna Wariya: Hukumar EFCC Ta Yi Karin Haske kan Shari'ar Yahaya Bello
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, na fuskantar tuhume-tuhume da hukumar EFCC ta shigar a kansa a kotu
- Hukumar EFCC ta bayyana cewa ba ta manta da shari'ar tsohon gwamnan na jihar Kogi ba domin lamarin yana gaban kotu
- Kakakin EFCC ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kogi ba mai laifi ba ne har sai idan kotu ta tabbatar da hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi magana kan shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
EFCC ta bayyana cewa ba a samu Yahaya Bello da laifi ba har sai kotu mai cikakken iko ta tabbatar da hakan.

Source: Twitter
Darektan hulda da jama'a na hukumar EFCC, Wilson Uwuajaren ya bayyana hakan yayin wata hira a shirin 'Morning Show' na tashar Arise tv a ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2025.
Ina aka kwana kan shari'ar EFCC da Yahaya Bello?
Hukumar ta jaddada cewa ana ci gaba da shari’ar da ake yi wa Yahaya Bello, kuma kotu ce kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan ko yana da laifi ko a’a, ba EFCC ba.
Wilson Uwuajeren ya bayyana cewa gurfanar da mutum a gaban kotu kan aikata manyan laifuffuka na cin lokaci, domin ana bukatar gabatar da shaidu da hujjoji a gaban kotu.
Uwuajeren ya ce a halin yanzu EFCC na ci gaba da gurfanar da shari’ar ta hanyar gabatar da shaidu da hujjoji, yana mai jaddada cewa hukuncin karshe yana hannun kotu gaba ɗaya.
Ana ci gaba da shari'ar Yahaya Bello
Ya kuma bayyana cewa bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, duk wanda ake yi wa shari’a ana ɗaukarsa a matsayin mara laifi har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.
Ya sake jaddada kudirin hukumar na tabbatar da adalci ga bangaren masu gabatar da kara da kuma bangaren masu ba da kariya, yana mai cewa babu wani abu da ya samu matsala ko kauce hanya wajen tafiyar da shari’ar.
“Abu guda da ya kamata mutane su fahimta shi ne yadda gurfanar da shari’ar aikata laifi ke tafiya a Najeriya. Yana ɗaukar lokaci kafin a tabbatar da wasu abubuwa a gaban kotu. Har zuwa yanzu, ana ci gaba da shari’ar a gaban kotu."
“Muna gabatar da shaidu, mun gabatar da hujjoji. Ba hukumar EFCC ba ce za ta yanke hukunci, kotu ce za ta yanke hukunci. Abin da ya rataya a wuyanmu shi ne mu bi tsarin shari’a yadda ya kamata domin tabbatar da adalci ga kowane bangare.”
“Yahaya Bello a halin yanzu yana gaban shari’a, amma kundin tsarin mulki ya tanadi cewa duk wanda ake yi wa shari’a ana ɗaukar sa a matsayin mara laifi har sai kotu ta tabbatar da akasin haka."
"Don haka duk abin da jam’iyyarsa ke yi masa lamari ne na cikin gida, ba ya da alaƙa da EFCC ko tuhume-tuhumen da muka shigar a gaban kotu.”
“Abin da jam’iyya za ta yi da Yahaya Bello lamari ne na jam’iyya. EFCC ba jam’iyyar siyasa ba ce. Ba mu da sha’awar siyasa. Mu hukuma ce ta tabbatar da bin doka, kuma abin da muke yi ke nan.”
- Wilson Uwuajaren

Source: Facebook
EFCC ta yi wa Gwamna Bala martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta ragargaji gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa zarge-zargen da gwamnan na Bauchi ya yi, babu kamshin gaskiya a cikinsu.
Ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a zarge-zargen kuma ta jaddada cewa ita hukuma ce mai cin gashin kanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


