Lokaci Ya Yi: Tsohon Kwamishinan Ilimi Ya Rasu Yana da Shekaru 78 a Jihar Kaduna
- Tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Alhaji Suleiman Lawal Kauru, ya rasu yana da shekaru 78 a asibitin Shika da ke Zaria
- Jana'izar marigayi Jarman Kauru ta samu halartar manyan sarakuna da tsohon gwamna Mukhtar Ramalan Yero a dandalin Filin Mallawa
- Marigayin ya taba zama shugaban makarantar Nuhu Bamalli sannan ya rike mukaman gwamnati daban-daban dake da alaka da ilimi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - An gudanar da jana'izar tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Alhaji Suleiman Lawal Kauru, a birnin Zaria.
Alhaji Suleiman, wanda ya rasu yana da shekaru 78 a duniya, ya riga mu gidan gaskiya ne a daren ranar Asabar, 3 ga watan Janairu, 2026.

Source: Facebook
Tsohon kwamishina a jihar Kaduna ya rasu
Rahoton Radio Nigeria ya nuna cewa Alhaji Suleiman ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, bayan ya shafe lokaci mai tsawo yana fama da jinya.
Hakazalika, ya rasu ya bar mata biyu, 'ya'ya da dama, da kuma jikoki. A cikin 'ya'yansa akwai Alhaji Nuraddeen Suleiman Lawal Mayana Kauru, sakataren ilimi na kwalejin Nuhu Bamalli, Zaria.
An gudanar da sallar jana'izarsa a Filin Mallawa da ke Tudun Wada, Zaria, inda manyan baki suka halarta, kamar yadda rahoto ya nuna.
Daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar har da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, Mai Martaba Sarkin Kauru, Alhaji Ya'u Shehu Usman, wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau, da kuma tsofaffin kwamishinoni da jami'an gwamnati na yanzu.
Tarihin ayyukan tsohon kwamishinan Kaduna
Marigayin ya kasance babban amini ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Namadi Sambo da kuma Sanata Aliyu Magatarda Wamakko.
Alhaji Suleiman Lawal, wanda shi ne Jarman Kauru, ya taka rawar gani sosai a ɓangaren ilimi da shugabanci a Najeriya in ji rahoton jaridar Daily Trust.
Ya taɓa riƙe muƙamin shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria, sannan ya yi kwamishinan ilimi na jihar Kaduna.
Haka kuma, ya wakilci jihar Kaduna a hukumar FCC sannan ya kasance mamba a majalisar gudanarwa ta jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria a shekarar 2013.

Kara karanta wannan
Ana rade radin komawa APC, mataimakin gwamnan Kano ya tura sako ga Abba da Kwankwaso

Source: Original
An yaba da sadaukarwa tsohon kwamishina
Har zuwa mutuwarsa, marigayin shi ne sakataren kwamitin gina asibitin koyarwa na ABUTH da ke Shika da kuma asibitin idanu na ƙasa da ke Kaduna.
Yaransa da abokan aikinsa sun bayyana shi a matsayin mutum mai hazaƙa, dattijo, kuma uba ga kowa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaban ilimi da horas da malamai.
Lawal Jibril Sani, ɗaya daga cikin ɗalibansa, ya bayyana shi a matsayin jagora mai fasahar magana da kuma zurfin ilimi wanda tarihi ba zai taɓa mancewa da shi ba.
Sarkin Kauru ya zama Amirul Hajj
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nada Mai Martaba Sarkin Kauru, Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj na 2025.
Hakan na nufin Sarkin Kauru, Alhaji Ya'u ne ya jagoranci maniyyatan jihar Kaduna a sauke farajin aikin Hajji na shekarar 2025 da gudanar a kasa mai tsarki.
An ce an yi la’akari da jajircewar basaraken wajen yi wa al’umma hidima, tsantsar gaskiya, da kuma irin kwarewarsa a bangaren shugabanci da tafiyar da al’amuran jama’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
