Wata Sabuwa: Likitoci Sun Sanya Ranar da Za Su Koma Yajin Aiki a Fadin Najeriya
- Kungiyar likitoci ta NARD ta ayyana ranar 12 ga watan Janairu a matsayin ranar fara yajin aikin gama-gari a fadin Najeriya baki daya
- Likitocin sun bayyana cewa gwamnati ta gaza cika yarjejeniyar da suka kulla a baya, wanda hakan zai janyo janyewar ayyuka a dukkan asibitoci
- Shugaban kungiyar ya ce ba za su taba janye yajin aikin ba har sai gwamnati ta biya dukkan bukatun su da suka jima suna neman a biya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewar aiki ta ƙasa (NARD) ta sanar da shawarar da ta ɗauka na komawa yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar nan.
Likitocin sun ce daga ranar 12 ga watan Janairun shekarar da muke ciki, mambobin kungiyar za su janye aiki daga kowanne asibiti na fadin Najeriya.

Source: Twitter
Likitoci za su tsunduma yajin aiki
Wannan mataki na zuwa ne sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika yarjejeniyar da aka cimma a baya (MoU) game da jin daɗin ma'aikatan lafiya a cewar rahoton Channels TV.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Mohammad Suleiman, ya tabbatar da wannan mataki bayan wani taron gaggawa na majalisar zartarwa da aka gudanar ranar Juma’a.
Likitocin sun bayyana cewa za su tsunduma yajin aikin, sakamakon watsi da gwamnati ta yi da kukan su duk da gargaɗin da suka bayar a baya.
Hakazalika, likitocin sun yanke shawarar gudanar da taron manema labarai guda 91 cikin kwanaki bakwai domin sanar da duniya halin da suke ciki.
Likitoci za su gudanar da zanga zanga
NARD ta kuma ba da umarnin gudanar da zanga-zangar lumana a dukkan asibitoci 91 da ke ƙarƙashin ƙungiyar a faɗin ƙasar nan.
Kungiyar ta shirya gudanar da zanga-zangar a matakin asibitoci daga ranar 12 zuwa 16 ga watan, sannan daga baya a gudanar da wata gagarumar zanga-zangar ƙasa.
Dr. Suleiman ya jaddada cewa ba za su janye yajin aikin ba har sai gwamnati ta aiwatar da mafi ƙanƙancin buƙatun da suka gabatar mata na inganta yanayin aiki da biyan haƙƙoƙin su.

Source: Getty Images
Halin da za a iya shiga a fadin kasa
Wannan mataki zai jefa harkar lafiya ta ƙasa cikin wani hali na daban, musamman a daidai lokacin da marasa lafiya ke buƙatar kulawa a asibitocin gwamnati.
Majalisar zartarwa ta NARD ta buƙaci mambobinta su kasance masu juriya da haɗin kai a cikin wannan fafutuka ta neman haƙƙi.
Ƙungiyar ta ce dole ne gwamnati ta nuna da gaske wajen magance matsalolin likitoci domin dakile rushewar sashen kiwon lafiya a Najeriya.
'Akwai bukatar gwamnati ta cika alkawari' - Dr. Shamsu
A zantawarmu da Dr. Shamsu Muhammad daga jihar Katsina, ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta nuna damuwarta kan halin da kiwon lafiya yake ciki, ta hanyar cika alkawarin da ke a yarjejeniyar da ta cimma wa da NARD.
Dr. Shamsu ya ce:
"Ya zama wajibi ga gwamnati ta cika bukatun likitocin gaba ɗaya yanzu da suke barazanar shiga wani sabon yajin aiki.

Kara karanta wannan
Dalibai za su mamaye Aso Rock, an sanya ranar zanga zangar adawa da harajin Tinubu
"Batutuwa kamar ƙarancin walwala, bashin albashi, da kuma matsalar hijirar likitoci zuwa kasashen waje na ci gaba da jawo tabarbarewar kiwon lafiya a kasar nan.
"Biyan bukatun likitocin shine kawai hanyar riƙe ƙwararrun likitoci da kuma gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga dukkan 'yan ƙasa.
"Yajin aikin da ke faruwa akai-akai na haifar da mummunar illa ga marasa lafiyar Najeriya waɗanda suka dogara ga asibitocin gwamnati kawai.
"Ana dakatar da manyan tiyata, ana rufe dakunan shan magani, kuma aikin yau da kullum na tsayawa. Wannan na haifar da tabarbarewar lafiya da ma mutuwar marasa lafiya da za a iya kauce masu."
Dr. Shamsu ya ce yanzu ya kamata gwamnati ta ba da fifiko ga yarjejeniyar da ta cimmawa da likitocin da kuma daukar duk matakan da suka dace don inganta walwalar ma'aikatan lafiya.
Bukatun likitoci ga gwamnatin tarayya
Tun da fari, mun ruwaito cewa, kungiyar likitocin NARD sun zayyano bukatu 19 da suke neman gwamnatin tarayya ta cika masu, ko su shiga yajin aiki.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Muhammad Suleiman, ya bayyana cewa yajin aikin ya zama dole sakamakon gazawar gwamnati wajen cika alkawuran da ta sha yi.
Likitocin sun gabatar da bukatu 19 ga gwamnati ciki har da neman karin albashi, gyaran asibitoci, da inganta yanayin aiki, wadanda suka ce wajibi ne a cika su.
Asali: Legit.ng

