Babbar Kotun Tarayya Ta Shirya Zama kan Bukatar da Abubakar Malami Ya Shigar gabanta

Babbar Kotun Tarayya Ta Shirya Zama kan Bukatar da Abubakar Malami Ya Shigar gabanta

  • Tsohon ministan shari'a kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN) na ci gaba da neman a sake shi daga gidan yari
  • Rahotanni sun nuna cewa babbar kotun tarayya mai zama a Abuja za ta yi zama domin sauraron bukatar beli da Malami ya shigar gabanta
  • Hukumar EFCC ta gurfanar da Malami, dansa da wata da aka bayyana da matarsa a gaban kuliya kan zargin safarar kudi da suka kusa Naira biliyan 9

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja za ta yi zama domin sauraron bukatar belin tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

Abubakar Malami, SAN, wanda Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar a kotu, na tsare a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.

Kara karanta wannan

An fitar da tambarin sabuwar hukumar haraji ta Najeriya bayan Tinubu ya rusa FIRS

Abubakar Malami.
Tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta tattaro vewa, Malami, babban lauya a Najeriya da ya kai matsayin SAN, na fuskantar shari'ar almundahana tare da ɗansa Abdulaziz da ɗaya daga matansa, Bashir Asabe.

EFCC ta gurfanar da Malami da dansa

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a gaban kotu kan zargin safarar kudade ta haramtacciyar hanya.

Idan baku manta ba, hukumar EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 16 kan Malami, dansa da kuma Hajia Asabe

An zarge su da satar kudi har Naira biliyan 8.7, amma kuma su duka sun musanta aikata laifuffukan da ake tuhumarsu lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotu a ranar 29 ga Disamba, 2025.

Bayan sauraron karar, kotun tarayya ta umarci a tsare Malami da sauran wadanda ake tuhumarsu tare a gidan gyaran halin Kuje.

Kotu ta umarci a tsare Malami a Kuje

Alƙalin kotun, Mai Shari'a Emeka Nwite, ya ba da umarnin a tsare su har zuwa lokacin da za a saurari tare da yanke shawara kan neman belin da lauyoyinsu suka yi, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Peter Obi maraba zuwa ADC, ya fadi amfanin shigarsa jam'iyyar

A zaman da ya gabata, lauyan wadanda ake kara, Joseph Daudu (SAN), ya yi ƙoƙarin neman belin su, amma kuma lauyan EFCC, Ekele Iheneacho (SAN), ya gabatar da hujjojin adawa da hakan.

Abubakar Malami.
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami tare da jami'an EFCC a harabar kotu Hoto: @EFCCNigeria
Source: Twitter

Mai Shari'a Emeka Nwite ya dage zaman shari'ar bayan sauraron hujjojin kowane ɓangare domin nazarin takardun neman belin wadanda ake kara.

A halin yanzu, babbar kotun tarayya za ta yi zama a Abuja yau Juma'a, 2 ga watan Janairu, 2026 domin duba yiwuwar ba da belin Malami da sauran wadanda EFCC ke tuhuma.

Yadda aka ba da belin Malami a baya

A wani rahoton, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon Antoni Janar kuma ministan shari'a Abubakar Malami (SAN).

Mai shari'a Bello Kawu ne ya amince da buƙatar belin a ranar Talata, biyo bayan wani koke da lauyoyin Malami suka shigar gabansa.

Alkalin kotun ya bayyana cewa ya amince da belin ne saboda dalilai na fuskantar tsananin kunci da wanda ake ƙara yake yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262