Tashin Hankali: An Kashe Bayin Allah Ana Tsaka da Murnar Shiga 2026 a Garin Jos

Tashin Hankali: An Kashe Bayin Allah Ana Tsaka da Murnar Shiga 2026 a Garin Jos

  • Manoma tara ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu mahara sun kai farmaki kauyen Bum da ke Jos ta Kudu a daren ranar Laraba
  • Harin ya faru ne duk da cewa an bayar da rahotannin sirri na harin, wanda ya yi sanadiyyar daidaita daukacin wani iyali a Bum
  • Shugabannin yankin sun koka kan yadda jami'an tsaro suka kasa dakile harin da ya faru lokacin da mutane ke tsaka da barcin dare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Wani mummunan hari da aka kai ƙauyen Bum da ke ƙarƙashin gundumar Chugwi, a yankin Vwang na ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla manoma tara.

Wannan harin ya faru ne a daren ranar Laraba, 31 ga watan Disamba, 2025, da misalin ƙarfe 11:00 na dare, a daidai lokacin da duniya ke murnar shiga sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda 30 sun mamaye ofishin 'yan sanda, sun kona shi kurmus

'Yan bindiga sun kashe manoma a jihar Filato
Taswirar jihar Filato da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe bayin Allah a Filato

Maharan sun kutsa cikin ƙauyen tare da buɗe wuta ba kakkautawa lokacin da mutane ke barci, lamarin da ya jefa yankin cikin firgici da baƙin ciki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren gundumar Vwang, Iliya Chung, ya tabbatar da cewa lamarin ya raba iyalai da dama da masoyansu.

A cewarsa, an fara gano gawarwakin mutane shida ne tun da daddare, amma zuwa safiyar ranar Alhamis, 1 ga watan Janairu, 2026, adadin waɗanda suka mutu ya kai tara.

Abin baƙin ciki shi ne yadda harin ya shafi maza, mata, har da ƙananan yara, inda akwai wani gida da aka kashe gaba daya mutanen gidan.

An ba jami'an tsaro rahoton sirri kafin harin

Wannan hari ya zo ne a matsayin babban kalubale ga tsaro a jihar, musamman a wannan lokaci na bukukuwan sabuwar shekara.

Kakakin ƙungiyar matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya bayyana cewa wannan harin ya afku ne duk da cewa an daɗe ana samun rahotannin sirri da ke gargaɗin cewa wasu ƙauyuka a Jos ta Kudu suna fuskantar barazanar hare-hare.

Kara karanta wannan

Jirgi ya yi hatsari dauke da fasinjoji a Najeriya, fiye da mutane 5 sun mutu

Ya soki yadda jami’an tsaro suka kasa ɗaukar matakin gaggawa domin dakile wannan kisan kiyashi, in ji rahoton Business Day.

A halin yanzu, mazauna yankin suna gudanar da ayyukan bincike da ceto domin tabbatar da ko akwai wasu da suka ji rauni ko kuma waɗanda suka ɓace a cikin daji yayin gudun ceton rai.

Rahoto ya nuna cewa an sanar da jami'an tsaro yiwuwar kai harin, amma ba su dauki mataki ba.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

An zargi jami'an tsaro da kin daukar mataki

Duk da cewa an riga an sanar da rundunar ‘yan sandan Plateau da kuma rundunar haɗin gwiwa ta Operation Enduring Peace game da wannan hari, har yanzu hukumomin ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Wannan shiru na hukumomin tsaro ya ƙara fusata mazauna yankin waɗanda ke ganin ana barin su cikin haɗari ba tare da kariya ba.

Wannan harin ya sake farfaɗo da fargabar rikicin manoma da makiyaya a jihar Plateau, wanda ya daɗe yana ci wa jihar tuwo a ƙwarya.

Gwamnan Filato ya fice daga PDP

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya kore dukkan jita-jitar da ake yadawa na barin jam'iyyar PDP mai mulki a jihar.

Kara karanta wannan

Bam a masallaci: Wanda ake zargi ya fadi makudan kudi da aka ba shi a Borno

Caleb Mutfwang ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, yana cewa yana bukatar shugabanci mai maida hankali da ingantaccen aiki.

A wasikar da ya rubuta ranar 29 ga Disamba, 2025, Mutfwang ya sanar da shugaban PDP na mazabarsa cewa ya janye daga jam’iyyar nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com