'Abubuwa 6 da Musulmi Zai Yi Ya Shiga Aljanna,' Daurawa Ya Aiko Saƙo daga London
- Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana ayyuka guda shida da Manzon Allah ya lamunce wa duk wanda ya kiyaye su shiga gidan Aljanna
- A cewarsa, Annabi ya jaddada cewa, idan mutum ya kiyaye abubuwan, ciki har da rikon amana, fadin gaskiya, to ba shakka zai shiga Aljanna
- Malamin ya kuma yi kira ga Musulmi da su kasance masu danne fushi da yafiya, domin hakan na cikin siffofin muminai na kwarai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Landan - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sake tunatar da Musulmi wani albishir da Manzon Allah (SAW) ya yi wa masu son shiga Aljanna.
Sheikh Aminu Daurawa ya ce Annabi Muhammad (SAW) ya kawo wasu ayyuka shida, da suka zama lamini ga Musulmi ya shiga Aljanna idan an je lahira.

Source: Facebook
Abubuwa 6 da yinsu zai kai mutum Aljanna
A cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, malamin ya ce:
"Annabi Muhammad (SAW) ya ce, ku lamunce mun abubuwa guda shida, ni kuma zan lamunce maku shiga Aljanna."
Sheikh Daurawa, ya jero abubuwan guda shi da suka hada da:
- Ku yi gaskiya idan za ku yi magana.
- Ku cika alkawari idan kun dauka.
- Ku rike amana idan an amince maku, an ba ku amana.
- Ku kiyaye mutuncin ku.
- Ku iyaye idanuwanku.
- Ku kiyaye hannayenku.
Sheikh Daurawa ya ce Annabin Rahama ya jaddada cewa wanda ya kiyaye wadannan abubuwa shida, to an lamunce masa shiga Aljanna.
Sharhin da Sheikh Daurawa ya yi
Fitaccen malamin, ya ce wadannan abubuwan shida, suna nan a cikin Al-Kur'ani, da kuma ingantattun Hadisan Manzon Allah (SAWA).
"Allah ya ba mu ikon kiyayewa, Allah ya sa mu 'yan Aljanna ne ba 'yan wuta ba ne."
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Legit Hausa ta fahimci cewa Sheikh Daurawa ya aiko da wannan sakon bidiyon ne makonni biyu da suka gabata, a lokacin da ya ke birnin London.
Malamin addinin, ya yi wa bidiyon take da 'Nasiha hudu daga London" da kuma "Laminin shiga Aljannah guda 6."
Kalli cikakken bidiyon a nan kasa:
Nasiha ta 3 daga Sheikh Daurawa
Kafin malam ya fitar da wannan nasiha ta hudu, ya fitar da nasiha ta uku daga London mai taken 'kada ka yi fushi,' inda a cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce:
"Fushi wani hali ne da ake yabonsa a wani lokaci, ake kuma zarginta a wasu lokutan. Idan mutum ya yi fushi a inda ya kamata ya yi fushi za a yaba masa, amma idan ya yi fushi a inda bai kamata ba, za a zarge shi."
Sheikh Daurawa ya ce fushi ya zo a wurare 24 kuma a sigogi daban daban a cikin Al-Kur'ani, kuma Allah ya siffanta muminai da 'masu yin fushi' amma 'masu yafiwa da hadiye fushin.'
Kalli cikakken bidiyon a nan kasa:

Source: Youtube
Mutane sun yi godiya ga Sheikh Daurawa
kannywood__update:
"Allah ka barmu da Manzon Allah."
jaoji_online:
"Allahumma Salli Wa Sallim Ala Nabiyyina Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallim."
mohammedjamiluahmed:
"Jazakalluhu khairan, Allah (SWA) ya karawa malan lafiya, ya jikan mahaifa, ya sa a gama lafiya."
faisaljr337:
"Muna godiya malam. Allah ya sa mu dace alfarmar Manzon Allah."
moh_lawan1:
"Wannan gaskiya ne malam, Allah ya saka da alheri."
Abubuwan da ake so a yiwa iyaye bayan rasuwarsu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Sheikh Aminu Daurawa ya tunatar da daukacin 'ya'ya nauyin da ya rataya a wuyansu yayin da mahaifinsu ya kwanta dama.
Fitaccen malamin addinin ya ce akwai abubuwa biyar da ake so mutum ya yi wa mahaifinsa idan ya rasu domin sama masa rahama a yayin da ya ke kwance a kabari.
A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce abu na farko da ake so 'ya'ya su yiwa mahaifinsu bayan rasuwarsa shi ne addu'a.
Asali: Legit.ng


