Rundunar Sojoji Ta Fara Fitar da Bayanai kan Harin da Amurka Ta Kai Jihar Sakkwato

Rundunar Sojoji Ta Fara Fitar da Bayanai kan Harin da Amurka Ta Kai Jihar Sakkwato

  • Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta fara bayanin nasarar da aka samu kan yan ta'adda a farmakin da Amurka ta kai jihar Sakkwato
  • Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Michael Onoja ya bukaci jama'a su guji taimaka wa 'yan ta'ddar da harin Amurka ya tarwatsa
  • Ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa rundunar sojin Najeriya na ci gaba da kokarin tattara barnar da aka yi wa yan ta'adda kuma za ta fitar da bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Hedkwatar Sojoji ta Ƙasa (DHQ) ta sake jaddada nasarar farmakin da Amurka ta jagoranta kan sansanonin ’yan ta’adda a jihar Sakkwato.

Hedkwatar sojojin Najeriya ta bayyana harin da Amurka ta kawo a matsayin wanda aka yi bisa sahihan bayanan sirri kuma mai matuƙar tasiri.

Sojojin Najeriya.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a cikin daji Hoto: DHQ Nigeria
Source: Twitter

Haka kuma, ta gargadi al’umma da su guji ɓoye ko taimaka wa ’yan ta’addan da ke tserewa bayan sun ji ruwan bama-bamai, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun gwabza fada da 'yan ta'adda a Borno, an lalata sansanoni 3

Daraktan Yaɗa Labarai na DHQ, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan ayyukan sojoji na 2025.

Wace nasara aka samu a harin Amurka?

Janar Onoja ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike tare da tantance barnar da harin Amurka ya yiwa yan bindiga a Sakkwato, inda ya ba da tabbacin cewa za a fitar da bayanai da zarar an kammala.

“A halin yanzu, muna ba jama’a shawara su dogara da bayanan da fadar shugaban ƙasa da ministan harkokin wajen suka fitar," in ji shi.

Janar Onoja ya tabbatar da cewa bayanan sirri sun nuna a fili cewa ’yan ta’adda suna cikin wuraren da Amurka ta jefa bama-bamai a Najeriya tun kafin kai harin.

Ya ƙara da cewa an kai harin bisa ingantattun bayanan da aka samu, ko da yake ba a bayyana wasu bayanai ba saboda dalilai na tsaro.

Shin Amurka ta kai hari jihar Kwara?

Dangane da fashewar wani abu a Offa, Jihar Kwara, kakakin sojojin Najeriya ya ce bincike ya nuna cewa lamarin na iya zama sakamakon kuskuren ɗan Adam ko na na’ura, inda ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

“Muna kara gode wa Allah saboda babu wanda ya rasa ransa amma duk da haka muna ci gaba da bincike,” in ji shi.

Janar Onoja ya ce sojoji sun kara kaimi a fannin tattara bayanan sirri da tsara ayyukan tsaro a faɗin ƙasar nan domin hana ’yan ta’addan da harin ya tarwatsa shiga cikin al’umma.

“Muna sa ido kan motsinsu a duka kewayen wuraren da aka kai harin, kuma mun sanar da dukkan kwamandojin rundunonin tsaro domin su sa ido. Manufarmu ita ce hana ’yan ta’adda cakudawa da al’umma,” in ji shi.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Janar Onoja ya jaddada muhimmancin haɗin kan jama’a, inda ya bukaci ’yan ƙasa da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi, yana mai cewa tsaro nauyi ne na kowa, in ji rahoton Vanguard.

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Borno

A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar sojoji ta Operation Hadin Kai sun samu gagarumar nasara a fafutukar yaƙi da ta’addanci a jihar Borno.

Sojojin tare da haɗin gwiwar dakarun sa-kai, suka yi wa yan ta'addan Boko Haram/ISWAP kwanton ɓauna a yankin Ladantar da ke ƙaramar hukumar Bama.

Ana zargin 'yan ta'addan sun fito ne da jirgin domin yin leƙen asiri kan ayyukan sojoji da mazauna yankin kafin su kai farmaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262