Gwamna Ya Samu Bayanan Sirri, Ya Gano Shirin da 'Yan Bindiga Suka Yi na Kawo Farmaki
- Gwamnatin jihar Kwara ta ce bayanan sirri sun tabbatar da cewa miyagun 'yan bindiga sun shirya kai hare-hare a sabuwar shekara
- Bisa haka, gwamnatin ta bukaci al'ummar jihar Kwara su yi taka tsan-tsan kuma su sanar da jami'an tsaro duk wani motsi da ba su yarda da shi ba
- Wannan dai na zuwa ne a lokacin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a jihar Kwara bayan wani hari da aka kai kan masu ibada a coci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara, Nigeria - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya yi gargadin cewa 'yan bindiga na shirin kai hare-hare a yayin ibadar cikar shekara da ake yi a coci-coci.
Gwamnan AbdulRazaq, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya bukaci jama'a su yi taka tsan-tsan kuma su sa ido kan mutanen da suke mu'amala da su.

Source: Facebook
Daily Trust ta tattaro cewa wannan gargadi na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinar sadarwa ta jihar Kwara, Bolanle Olukoju, ta fitar a ranar Laraba.
Gwamnatin Kwara ta gargadi jama'a
A cewarta, bayanan sirri sun nuna cewa wasu miyagu na shirin kai farmaki kan muhimman wuraren gwamnati da sauran wurare masu sauƙin kai hari.
Gwamnatin Kwara ta ce 'yan bindigan na wannan shiri ne domin ɗaukar fansa kan asarar da suka yi sakamakon hare-haren jami’an tsaro a baya-bayan nan, in ji Punch.
“Wannan gargaɗi ya zama dole ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa wasu miyagun mutane na shirin kai hari kan kadarorin gwamnati ko wasu wurare masu rauni,” in ji Olukoju.
Matakan da ya kamata mutane su dauka
Ta shawarci mazauna jihar Kwara da su rage tafiye-tafiyen da ba su da muhimmanci tare da guje wa tarukan jama’a da ka iya jefa su cikin haɗari a wannan lokaci na bukukuwa.
“Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan, su guji tafiye-tafiyen da ba su da muhimmanci, ko tarukan jama’a da ka iya zama abin hari ga masu garkuwa da mutane,” in ji sanarwar.
Gwamnatin Kwara ta kuma bukaci a ƙara taka-tsantsan a yayin ibadar cikar shekara da bukukuwan sabuwar shekara, tare da ba da tabbacin cewa za ta turo karin jami’an tsaro a sassan jihar.

Source: Twitter
“Muna kira ga jama'a da su zama masu sa ido sosai, musamman a yayin ibadar cikar shekara da hutun sabuwar shekara, jami’an tsaro za su zage dantse wajen kare rayuka da dukiyoyi,” in ji sanarwar.
Daga karshe, gwamnatin jihar Kwara ta bukaci jama’a da su rika sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da suke ganin ba su yarda da shi ba domin daukar matakin da ya dace.
Gwamnan Kwara ya ba 'yan ta'adda zabi 2
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya aika da sakon gargadi ga ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da ke aiki a jihar Kwara.
Gwamna Abdulrazaq ya gargade su da su fice daga jihar Kwara nan take ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani, wanda zai raba su da duniya.
Ya ce za a tura akalla jami'an tsaron dazuka 200 a kowace karamar hukuma domin tsaron dazuzzuka tare da taimaka wa ’yan sa- kai na yankunan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

