Ana Rade Radin Zai Koma APC, Gwamna Abba Ya Yi Jawabi bayan Sa Hannu kan Kasafin 2026
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar kasafin kudin 2026 a fadar gwamnatinsa da ke cikin birnin Kano
- Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da jita-jita ke kara karfi cewa gwamnan zai sauya sheka daga NNPP zuwa jam'iyyar APC
- Gwamna Abba ya yi jawabi kan kasafin kudin tare da bai wa mutanen Kano tabbacin aiwatar da shi yadda ya kamata domin inganta rayuwarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026 da Majalisar dokokin jihar ta amince da shi.
Gwamna Abba ya sa hannu a kasafin kudin, wanda ya kai Naira tiriliyan1.477 a daidai lokacin da ake yada jita-jitar cewa zai fice daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.

Source: Facebook
Jawabin da Gwamna Abba ya yi
Daily Trust ta ruwaito cewa da yake jawabi bayan sa hannu, Gwamna Abba ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da kasafin domin inganta rayuwar jama’a.
Ya bukaci mambobin majalisar zartarwarsa ta Kano da su ƙara ba gwamnati goyon baya tare da ƙwazo da jajircewa wajen aiwatar da manufofin ci gaba.
Ya bayyana cewa an samu nasarar aiwatar da kashi 80 cikin 100 na kasafin kuɗin 2025, wanda ya ce hakan ya kawo ci gaba a fannin gina ababen more rayuwa.
A cewar Gwamna Abba, kasafin kudin 2026 ya nuna fifikon da gwamnatinsa ke bai wa bangaren bunƙasa ababen more rayuwa da shirye-shiryen inganta rayuwar talakawa.
Gwamnan Kano ya dauki alkawari
Ya bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano, bayan nazari mai zurfi, ta ƙara kasafin daga N1.3trn zuwa N1.477trn.
Gwamna Abba ya yi alkawarin cewa za a yi amfani da duka kuɗaɗen da aka ware yadda ya dace, yana mai jaddada cewa al’ummar Kano za su amfana da manufofi da shirye-shiryen gwamnati ba tare da nuka banbanci ba.
“Kasafin da aka yi wa gyara ya ƙunshi muhimman buƙatu na bunkasa ababen more rayuwa, kuma mun shirya tsaf domin aiwatar da shi yadda ya dace don amfanin al’ummar Jihar Kano,” in ji Abba.

Source: Facebook
Yadda Majalisa ta amince da kasafin 2026
Tun da farko, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Ismail Falgore, ya bayyana cewa ‘yan majalisa sun yi zama da dukkan masu ruwa da tsaki kafin amincewa da kudirin kasafin ya zama doka.
Ya nuna kwarin gwiwar cewa idan aka aiwatar da kasafin yadda ya kamata, zai ƙara bunƙasa tattalin arziki da walwalar al’ummar Jihar Kano, kamar yadda Leadership ta kawo.
Majalisa ta gama karatu kan kasafin 2026
A baya, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kasafin kudin shekarar 2026, wanda zai lakume fiye da Naira tiriliyan 1.4.
Majalisa ta amince ne bayan kammala nazari kan kudirin kasafin da gwamnan Kano ya gabatar, tare da yi wa kasafin kudin karatu na uku wanda shi ne na karshe a doka.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin Kano, Hon. Husseini Lawan ya ce an samu karin sama da Naira biliyan 100 a kasafin kudin 2026.
Asali: Legit.ng

