Wike Ya Tsokano Jam'iyyar ADC, Ta Yi Masa Zazzafan Martani
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi martani bayan Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba ta da tasiri a jihar Rivers
- Mai magana da yawun jam'iyyar ADC a jihar Rivers, Cif Luckyman Egila, ya fito ya ragargaji Wike kan kalaman da ya yi
- Egila ya bayyana cewa Wike na yin maganganu ne saboda takaicin da yake yi kan kasa juya gwamnan jihar Rivers yadda yake so
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Jam’iyyar ADC reshen jihar Rivers ta yi wa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, martani bayan ya ce ba ta da tasiri.
Jam'iyyar ADC ta jaddada cewa Nyesom Wike, ba ya cikin kowace jam’iyyar siyasa, don haka ba shi da ikon magana a madadin kowace jam’iyya.

Source: Twitter
Mai magana da yawun ADC a jihar Rivers, Cif Luckyman Egila, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Leadership a birnin Port Harcourt a ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025.
Jam'iyyar ADC ta yi martani ga Nyesom Wike
Luckyman Egila ya mayar da martani kan kalaman baya-bayan nan da Wike ya yi na sukar jam’iyyar ADC a jihar Rivers.
Kakakin na ADC ya bayyana cewa a halin da ake ciki a yanzu, Nyesom Wike bai da jam'iyyar siyasa.
"Ba mu da niyyar mayar da martani ga Nyesom Wike, domin shi ba ya da jam’iyyar siyasa. Don haka ina mamakin daga inda yake magana. Kamar yadda kuka sani, ADC ita ce kadai jam’iyyar da shugaban kasa ke jin tsoronta.”
"Wike ya fito ya ce ADC ba ta da matsayi a jihar Rivers, wannan ba gaskiya ba ne. A zahiri, Wike ba ya cikin kowace jam’iyyar siyasa.”
"Wike mutum ne da ba shi da jam’iyya. Ina mamakin inda biyayyarsa take. Ya kamata a dora masa alhakin durkushewar jihar Rivers da ake gani a yau. Ina mamakin daga ina yake magana.”
- Nyesom Wike

Source: Facebook
Jam'iyyar ADC ta ce Wike na cikin takaici
Ya bayyana cewa yana ganin Wike na yin wadannan kalamai ne saboda takaici, yana mai cewa a halin yanzu Wike ba ya iya sarrafa gwamnan jihar Rivers kamar yadda ya saba yi a baya.
"Na yi amanna cewa yana magana ne saboda takaici, domin masu iko a yau sun riga sun fahimci cewa Wike ba zai iya sake sarrafa gwamnan jihar Rivers kamar yadda ya saba yi daga nesa ba.”
"Wannan matashin gwamnan ya farka daga barcinsa, kuma ya yanke shawarar shiga Jam’iyyar APC."
- Cif Luckyman Egila
Wike ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ba.
Nyesom Wike ya ce jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya za ta ruguje idan har ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya jaddada cewa har yanzu shi mamba ne a jam’iyyar PDP kuma ba ya da niyyar barinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

