Duk da Karancin Danyen Mai, NNPCL Ya Samu Ribar fiye da Naira Biliyan 502 a Wata 1

Duk da Karancin Danyen Mai, NNPCL Ya Samu Ribar fiye da Naira Biliyan 502 a Wata 1

  • Kamfanin NNPCL ya samu ribar Naira biliyan 502 a watan Nuwamba bayan duk da kalubalen da aka fuskanta na hakar danyen mai
  • Kudaden shigar kamfanin sun kai Naira tiriliyan hudu sakamakon ingantuwar samar da iskar gas da cinikayyar man fetur a cikin watan
  • An ce hakar danyen mai ya farfado zuwa fiye da ganga miliyan daya a kowace rana bayan raguwar da aka samu a watannin baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sanar da samun ribar da ta kai Naira biliyan 502 bayan cire haraji a watan Nuwamba na shekarar 2025.

Wannan gwaggwabar riba da kamfanin NNPCL ya samu na zuwa ne duk da ƙalubalen da aka fuskanta na raguwar hakar danyen mai.

Kamfanin NNPCL ya samu gwaggwabar ribar biliyoyin naira a watan Nuwamba
Sabon gidan sayar da man fetur mallakin kamfanin NNPCL. Hoto: @nnpclimited
Source: Twitter

NNPCL ya samu gwaggwabar riba a 2025

Kara karanta wannan

Kudin babura: EFCC ta gurfanar da jami'in gwamnati kan zargin handame N5.79bn

Rahoton kuɗi da ayyuka na kamfanin na watan Nuwamba wanda aka fitar a ranar Laraba, ya nuna cewa kamfanin ya samar da kudaden shiga har Naira tiriliyan 4.36, in ji jaridar Punch.

Nasarar da kamfanin ya samu ta dogara ne kacokan kan haɓakar samar da iskar gas da kuma ingantuwar hanyoyin jigilar mai, waɗanda suka taimaka wajen daidaita asarar da aka yi a ɓangaren hakar ɗanyen mai.

A watan Nuwamba, an sami matsakaicin hakar mai na ganga miliyan 1.36 a kowace rana, wanda hakan ke nuna farfaɗowa daga ganga miliyan 1.30 da aka rika samu a watan Oktoba, kodayake har yanzu bai kai ganga miliyan 1.77 da aka samu a farkon shekarar 2025 ba.

Yadda kamfanin NNPCL ya inganta samar da kudi

Wannan farfaɗowa da aka samu a watan Nuwamba ita ce ta farko bayan watanni uku a jere (Agusta zuwa Oktoba) ana samun raguwar hakar man.

NNPCL ya bayyana cewa ribar Naira biliyan 502 da ya samu ta biyo bayan ingantuwar cinikayya da kuma tabbatar da cewa bututun mai suna aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Kamfanin JED ya nemi masallatai da coci su rika biyan kudin lantarki a jihar Gombe

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa samar da iskar gas ya kai miliyan 6,968 a kowace rana, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gwaggwabar ribar kamfanin a daidai lokacin da ake fuskantar cikas a wasu rijiyoyin mai.

Kamfanin NNPCL ya zage damtse wajen samawa gwamnatin Najeriya kudaden shiga daga danyen mai
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari ya na jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @nnpclimited
Source: UGC

Rawar NNPCL a tattalin arzikin Najeriya

A dunkule, gudunmawar da NNPCL ta bayar ga asusun gwamnatin tarayya ta kai Naira tiriliyan 12.12 tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba 2025.

Wannan na nuna girman rawar da kamfanin ke takawa wajen samar wa gwamnati kuɗaɗen shiga a lokacin da ake buƙatar su, in ji rahoton ABN TV.

Duk da matsalolin da aka samu a layin Forcados da wasu rijiyoyin mai na Egbema, sabon tsarin kasuwanci na kamfanin da kuma rage kashe-kashen banza sun taimaka wajen dorewar wannan riba mai tsoka.

Gwamnoni sun dura kan kamfanin NNPCL

A wani labari, mun ruwaito cewa, sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin NNPCL da kamfanin Periscope Consulting, wanda gwamnoni suka dauka domin binciken wasu kudi.

Gwamnonin jihohin na zargin rashin tura dala biliyan 42.37 zuwa asusun Tarayya wanda ke neman zama matsala a tsakaninsu, lamarin da ya sa aka yi hayar masu bincike.

Rahoton FAAC na watan Nuwambar 2025 ya bayyana sababbin takaddamar, bayan an ruwaito cewa binciken zargin rashin tura kudaden ya kara tsawaita zuwa 2024.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com