Kwamishinan Abba Ya Fayyace a Matsayinsa a Sabanin Kwankwaso da Gwamnan Kano

Kwamishinan Abba Ya Fayyace a Matsayinsa a Sabanin Kwankwaso da Gwamnan Kano

  • Kwamishinan habaka kiwon dabbobi a Kano, Aliyu Isa Aliyu, ya bayyana matsayarsa a kan muhawarar siyasa da ke gudana a cikin tafiyar Kwankwasiyya
  • Masanin lissafin ya bayyana cewa a 'yan kwanakin nan, mabiya darikar Kwankwasiyya sun fuskanci kalubale iri-iri, musamman a wannan lokaci da siyasa ta yi zafi
  • A yayin da ya ke jaddada biyayyarsa ga Kwankwasiyya da girmamawarsa ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fadi inda ya fi karkata da ake batun canza sheka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kwamishinan habaka kiwon dabbobi a Kano, Aliyu Isa Aliyu ya yi bayani dalla-dalla kan matsayinsa game da muhawarar siyasar da ke gudana a cikin tafiyar Kwankwasiyya.

Wannan ya biyo bayan kiran da wasu ‘yan jam’iyyar NNPP ke yi na batun sauya shekar Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shiga APC: Kwankwaso ya gargadi masu shirin masa butulci a bidiyo

Kwamishina ya ce Kwankwaso uba ne gare su
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa mai tsawo, da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Aliyu ya bayyana ‘yan kwanakin nan a matsayin lokaci mai cike da ƙalubale ga ‘yan Kwankwasiyya.

Matsayar Kwamishina kan Kwankwaso da Abba

Sai dai tsohon malamin jami'ar ya ce ya zama dole ya fayyace dalilansa na goyon bayan tattaunawa kan yiwuwar sauya tsari a siyasance, domin kauce wa rikice-rikice a gaba.

Kwamishinan ya jaddada cewa har yanzu shi cikakken ɗan tafiyar Kwankwasiyya ne, tare da nuna girmamawa ga jagoran tafiyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ya bayyana Kwankwaso a matsayin uba a gare shi, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen gina rayuwarsa da tafiyarsa a siyasa.

Aliyu ya kuma yaba da gudunmawa da goyon bayan da ya samu daga Sanata Kwankwaso da kuma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya ce irin wannan ƙarfafawa ce ta taimaka masa a harkar siyasa.

Kara karanta wannan

An nada sabon shugaban NNPP a Kano, Gwamna Abba ya kafe sai ya tafi APC

Kwamishina a Kano ya goyi bayan a koma APC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf a wani taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa wasu sabbin matakan shari’a da suka shafi NNPP ne suka sanya shi sake tunani kan dambarwar da ake yi a yanzu.

Ya tuno cewa a ranakun 25 da 27 ga Nuwamba, 2025, Babbar Kotun Abuja ta hana INEC amincewa ko hulɗa da kowane ɓangare ta NNPP, sai tsagin da Agbo Gilbert Major ke jagoranta.

Kwamishina ya gargadi APC

A cewarsa, umarnin kotun da Mai Shari’a Bello Kawu ya bayar ya kuma hana INEC sa ido ko shiga cikin duk wani taron NNPP har sai an kammala shari’ar.

Aliyu ya yi gargaɗin cewa raina umarnin kotu na iya jefa jam’iyyar cikin manyan matsalolin doka, yana ambaton misalan zaɓukan Zamfara na 2019 da rikicin majalisun dokoki na Plateau a 2023.

Ya jinjina kokarin yan NNPP na kawo gwamnatin Kano mai ci, amma ya ce wasu masu ruwa da tsaki na ganin dacewar a binciki wasu hanyoyi da za su dawwamar da kwaniciyar hankali a jihar.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: 'Yan APC sun tattauna da Abba ba tare da Kwankwaso ba

Aliyu ya ƙara da cewa kiran sauya sheƙa ba don son rai ko buri na kashin kai ba ne, illa don wasu na ganin dabara ce ta daidaita Kano da gwamnatin tarayya domin samun kyakkyawar fahimta da cigaba.

Ya kuma jaddada cewa ba ya goyon bayan duk wani raini ga Sanata Kwankwaso, yana mai nuna kwarin gwiwa ga dogon dangantakar Madugu da Gwamna Abba Yusuf wadda ta shafe sama da shekaru 40.

"Ba sabani tsakanin Abba da Kwanwaso": Kwamanda

A baya, kun ji cewa Alhaji Abdulmajeed Ɗanbilki Kwamanda, babban jigo a APC, ya ce babu wani saɓani a tsakanin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da Rabi’u Musa Kwankwaso.

Dan Bilki ya bayyana haka ne a daidai lokacin da shugabannin ƙananan hukumomi ke neman Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso su koma jam’iyyar APC.

Abdulmajeed Ɗanbilki Kwamanda ya bayyana cewa Kwankwaso ne da kansa ya bayar da umarnin Abba ya koma APC, mataimakinsa zai ci gaba da zama NNPP domin duk inda ta fadi sha ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng