Peter Obi Ya Bi Sahun Atiku, a Hukumance Ya Bar LP zuwa Jam’iyyar ADC
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya tabbatar da ficewa daga jam'iyyar da ya yi mata takara a zaben 2023
- Peter Obi ya fice a hukumance daga jam’iyyar tare da komawa ADC da aka shirya domin hadaka game da zaben 2027
- Manyan jiga-jigan siyasa daga sassa daban-daban sun halarci taron kaddamar da ADC a Enugu da aka yi a karshen shekarar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar yayin wani taro.
Peter Obi ya tabbatar da ficewar tasa tare da komawa ADC jam’iyyar haɗin gwiwar wanda ƙungiyoyin siyasa suka halarta.

Source: Twitter
Peter Obi ya tabbatar da barin jam'iyyar LP
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya bayyana wannan matsaya a ranar Laraba 31 ga watan Disambar 2025 yayin wani taro da aka gudanar a Enugu, cewar TheCable.
Yayin taron da aka gudanar a Enugu inda aka kaddamar da dandalin siyasar haɗin gwiwar, Obi ya ce sun shirya tsaf domin zaben 2027.
Da yake jawabi a wajen taron, Obi ya ce:
“Mun kammala wannan shekara da fatan cewa a 2026 za mu fara tafiyar ceto al'ummarmu.
“Za mu yi adawa da maguɗin zaɓe ta kowace hanya da doka ta halatta a 2027.”
Obi ya kuma ja hankalin ‘yan Najeriya kan batun takardun makaranta, yana mai cewa har yanzu akwai damar shekara guda ga kowa ya tabbatar da sahihancin makarantun da ya halarta.
“Ba ma son mu koma kotu kuma a ce mana batun na cikin harkokin gaban zaɓe. Dole ne tsarin neman takara ya fara tun yanzu,”
- In ji Peter Obi

Source: Facebook
Manyan 'yan siyasa da suka tarbi Peter Obi
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron akwai shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, haka kuma, an ga tsohon gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal.
Sauran sun hada da tsohon mataimakin kakakin Majalisar Wakilai Emeka Ihedioha, da sanatoci da dama ciki har da Ben Obi, Victor Umeh, Tony Nwoye, Gilbert Nnaji, Enyinnya Abaribe, Sam Egwu, da sauran manyan ‘yan siyasa.
Zaman Obi a PDP da takara a zaben 2023
A baya dai, Peter Obi ya fice daga Jam’iyyar PDP a ranar 25 ga Mayu, 2022, yana mai cewa abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar ba su ba shi damar bayar da gudummawa mai ma’ana ba.
Bayan haka, ya shiga Labour Party a ranar 27 ga Mayu, 2022, inda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, amma ya zo na uku a sakamakon zaɓen.
Canza gidan Obi zuwa ADC na daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa da ke nuna yadda ake shirin tunkarar zaɓen 2027 a Najeriya, cewar Punch.
Tsohon Sanata ya sauya sheka zuwa ADC
Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta rasa daya daga cikin jiga-jiganta a jihar Enugu bayan ficewar tsohon sanata a majalisar dattawan Najeriya.
Sanata Gilbert Nnaji wanda ya wakilci Enugu ta Gabas ya fice daga jam'iyyar PDP bayan ya kwashe shekara 27 a cikinta.
Tsohon sanatan ya tattara kayansa zuwa ADC wadda ya bayyana a matsayin inda zai samu damar ba da gudunmawarsa wajen gina kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

