Bayan Korafe Korafe, Tinubu Ya Fadi Lokacin Fara Aiwatar da Dokar Haraji
- Gwamnatin tarayya ta shirya aiwatar da sababbin dokokin haraji wadanda ta ce za su kawo gyara a kasar nan duk da korafe-korafen jama'a
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya kan lokacin da za a fara aiwatar da sababbin dokokinn karbar harajin
- Mai girma Bola Tinubu ya nuna cewa sababbin dokokin ba a kirkiro ba su domin kara yawan harajin da 'yan Najeriya ke biya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan sababbin dokokin haraji, ciki har da wadanda suka fara aiki tun 26 ga watan Yuni, 2025.
Shugaba Tinubu ya ce sababbin dokokin da aka tsara za su fara aiki a 1 ga Janairu, 2026, za a aiwatar da su yadda aka tsara ba tare da jinkiri ba.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga, ya sanya a shafinsa na X.
Tinubu ya fadi lokacin aiwatar da dokokin haraji
Shugaba Tinubu ya ce dukkan korafe-korafen da aka gabatar an lura da su, amma ya kara da cewa ba a gano wata matsala mai karfi ba da za ta sa a dakatar ko a jinkirta tsarin gyaran haraji da ake aiwatarwa.
"Sababbin dokokin haraji, ciki har da wadanda suka fara aiki a ranar 26 ga Yuni, 2025, da sauran dokokin da za su fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, za su ci gaba kamar yadda aka tsara.”
"Wadannan gyare-gyare dama ce ta musamman wadda ke zuwa sau daya kacal domin kafa tubalin adalci kan harkar kudin shiga ga kasarmu.”
- Shugaba Bola Tinubu
Amfanin dokokin haraji ga al'ummar Najeriya
Shugaban kasar ya bayyana cewa dokokin harajin ba don kara haraji aka kirkiro su ba, sai dai domin gyara tsarin gaba daya, daidaita dokoki, kare mutunci tare da karfafa alakar da ke tsakanin gwamnati da al’umma.
"Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su goyi bayan matakin aiwatarwa, wanda yanzu ya shiga matakin aiwatarwa kai tsaye."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Tinubu na sane da korafe-korafe
Tinubu ya ce gwamnatinsa na sane da muhawarar jama’a game da zargin canje-canje a wasu sashe na sababbin dokokin haraji da aka amince da su kwanan nan.
“Ba a tabbatar da wata matsala mai girma ba da za ta bukaci katse tsarin gyaran. Amana ta gaskiya ana gina ta ne a hankali ta hanyar yanke shawarar da ta dace, ba ta hanyar gaggawar daukar matakai ba."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Twitter
Ya jaddada cewa gwamnatinsa na da cikakken kishin bin doka da oda da kuma kare mutuncin dokokin da aka kafa, yana mai alkawarin yin aiki tare da majalisar tarayya domin warware duk wata matsala da aka gano cikin gaggawa.
“Ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki bisa babban muradin jama’a, domin samar da tsarin haraji da ke kawo ci gaba."
- Shugaba Bola Tinubu
Majalisa ta bukaci dakatar da dokar haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta bukaci dakatar da aiwatar da sababbin dokokin haraji kan zargin an yi wasu sauye-sauye.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Hon. Kingsley Chinda, bayyana cewa wannan lamari babbar matsala ce a kundin tsarin mulki.
Hon. Kingsley Chinda ya yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na sauya dokokin da majalisa ta zartar, hari ne kai tsaye ga dimokuradiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


