Kotu Ta Yi Umarni a Kwace N1.1bn da ake Zargin na da Alaka da Gwamnatin Kano

Kotu Ta Yi Umarni a Kwace N1.1bn da ake Zargin na da Alaka da Gwamnatin Kano

  • Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ƙwace Naira biliyan 1.1 na wucin gadi da ake alaƙantawa da Gwamnatin Jihar Kano
  • Hukumar kokarin ana almundahana a Najeriya ta ICPC ta ce ana zargin kuɗin sun fito ne daga haramtattun ayyuka bayan ta zurfafa bincike
  • Kotun ta buƙaci a wallafa umarnin ƙwacen kudin na wucin gadi a jarida domin bai wa masu ruwa da tsaki damar kare kansu a kan zargin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin ƙwace Naira biliyan 1.1 na wucin gadi, kuɗin da ake zargin suna da alaƙa da Gwamnatin Jihar Kano.

A cewar kotun, buƙatar da ICPC ta gabatar abu ne da ya cancanci a duba, tare da bayar da umarnin a kwace kuɗin na wucin gadi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi karin haske game da zargin shirin yi wa ƴan adawa ɗauki ɗai ɗai

Kotu ta yi umarnin a kwace wasu kudi daga Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

The Nation ta wallafa cewa Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin a ranar Talata bayan amincewa da buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka (ICPC) ta shigar.

Kano: Kotu ta yi umarnin kwace wasu kudi

Daily Nigerian ta wallafa kotun ta umurci a wallafa umarnin ƙwacen kuɗin a cikin jaridar ƙasa domin bai wa duk wani mai ruwa da tsaki damar bayyana kansa, ya kuma nuna dalilin da ya sa bai kamata a ƙwace kuɗin ba.

An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga Janairu, 2026, domin kotu ta karɓi rahoto kan yadda aka aiwatar da umarnin wallafa sanarwar ƙwacen kuɗin.

A cewar takardun kotu, an gano kuɗin da adadinsu ya kai Naira biliyan 1.109 ne yayin binciken da aka fara sakamakon wata ƙorafi daga wasu mazauna Jihar Kano.

Ƙorafin ya yi zargin cewa an cire Naira biliyan 2.3 a tsabar kuɗi daga asusun rabon kudi na tarayya na jihar Kano da ke bankin UBA, sannan aka karkatar da su zuwa ayyukan da ba na gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damƙe ƴan ƙunar baƙin wake 2 kan tashin bam a masallacin Maiduguri

Yadda ICPC ta gano wasu kudi a Kano

A cikin wata rantsuwar shaida da David Nelson ya yi, ICPC ta bayyana cewa ana da kyakkyawan zargi an samu kuɗin sakamakon ayyukan haramun.

ICPC tana zargin an samo kudin daga asusun gwamnanti
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Masu bincike sun ce sun gano cewa izinin fitar da kuɗin ya fito ne daga Babban Akanta na Jihar Kano, Abdulkadir Abdulsalam, inda aka yi canja wurin kuɗin zuwa wasu kamfanonin canjin kudi guda biyu.

Hukumar ta ƙara da cewa an ɓoye mu’amalar ne ta hanyar bayyana kuɗin a matsayin biyan kuɗin dizal, bisa wasu wasiƙun izini da ake dangantawa da kamfanonin A. Y. Maikifi Oil & Gas da Ammas Petroleum.

Sai dai, darektocin gudanarwa na kamfanonin biyu sun shaida wa masu bincike cewa babu wata yarjejeniya ko isar da dizal da aka taɓa yi.

Kotu ta jikawa gwamnatin Kano aiki

A baya, mun wallafa cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Josephine Obanor, ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin Jihar Kano ta shigar kan hukumar ICPC.

Kara karanta wannan

Malami: Kotu ta iza ƙeyar surukin Buhari da ɗansa zuwa gidan yarin Kuje

Gwamnatin Kano ta shigar da kara domin hana Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) gudanar da bincike kan zargin almundahanar kuɗin tallafin karatu da aka ce an ware don daliban jihar.

Wasu jami’an gwamnatin Kano ne suka garzaya kotu suna neman a dakatar da ICPC daga ci gaba da binciken, bayan hukumar ta fara yunkurin bincike kan tsarin tallafin karatu na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng