Sojoji Sun Damƙe Ƴan Ƙunar Baƙin Wake 2 kan Tashin Bam a Masallacin Maiduguri

Sojoji Sun Damƙe Ƴan Ƙunar Baƙin Wake 2 kan Tashin Bam a Masallacin Maiduguri

  • Dakarun rundunar OPHK sun cafke mutane biyu da ake zargi da kai harin kunar bakin wake a Borno da Yobe
  • Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sun kuma samu nasarar dakile hanyoyin jigilar kayayyakin fashewa da ke tallafa wa Boko Haram a yankin
  • Rundunar ta ƙarfafa matakan tsaro a masallatai da kasuwanni a Maiduguri bayan harin da ya kashe bayin Allah da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun samu gagarumar nasara a ayyukan tsaro a jihohin Borno da Yobe, bayan cafke mutane biyu da ake zargi da shirya hare-haren kunar bakin wake a yankin .

Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin sun kuma yi nasarar tarwatsa muhimman hanyoyin dabaru da ke ciyar da ayyukan ta’addancin Boko Haram gaba.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta cafke fiye da mutane 3,000 a Kano, kwamishina ya yi bayani

An kama wasu da ake zargin ƴan ƙunar baƙin wake ne
Wasu daga cikin ƴan ta'addan da suka amsa sun shirya kai hari Borno da Yobe Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin an cafke shi ne a garin Banki, yayin wani hadin gwiwar sintiri da ayyukan tattara bayanan sirri.

An kama ɗayan kuma tun da farko a Damaturu, jihar Yobe, bisa alaƙa da harin kunar bakin wake da ya auku a Masallacin Kasuwar Gamboru a ranar 24 ga Disamba 2025.

An gano shirin ƴan ta'adda a Borno da Yobe

Rahotanni sun nuna cewa wasu rassan ‘yan ta’addan JAS da JNIM sun haɗa kai domin kai hare-haren kunar bakin wake da kuma amfani da na’urorin fashewa a wasu sassan Arewa maso Gabashin Najeriya.

An ce wata tawagar Boko Haram ƙarƙashin jagorancin wani fitaccen ƙwararren mai haɗa ban mai suna Munzir Abu Ziyadah.

Ƴan ta'addan sun shirya kai hare-hare har guda 10 na na’urorin fashewa da ake ɗaure wa jiki (PBIED), daga yankin sansanin Ali Ngulde.

Kara karanta wannan

Malami: Kotu ta iza ƙeyar surukin Buhari da ɗansa zuwa gidan yarin Kuje

Sun ratsa tsaunukan Ngoshe zuwa Gazuwa da Ngom, suna kutsawa al’ummomi da dama a Borno gabanin hare-haren da suka shirya don cutar jama'a.

Daga bisani, ɗaya daga cikinsu ya tayar da bam a Masallacin Kasuwar Gamboru a ranar 24 ga Disamba, lamarin da ya yi sanadin rasuwar Masallata biyar tare da jikkata wasu 32.

An tsaurara tsaro a Borno bayan harin Maiduguri

Bayan fashewar bam din a Maiduguri, Kwamandan Rundunar Ayyuka ta JTF Arewa maso Gabas, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayar da umarnin sauya salo.

An canja taki da sintirin yau da kullum zuwa dabarun farauta da kai hare-haren rigakafi domin dakile barazanar. An mai da hankali kan ayyukan da ke dogaro da bayanan sirri, ƙarfafa tsaro a masallatai da kasuwanni, tare da tsaurara kula da hanyoyin zirga-zirga a Maiduguri.

Harin Maiduguri ya gigita jama'a
Jami'an da suka kai dauki bayan harin masallacin Maiduguri Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

A ranar 29 ga Disamba, 2025 dakarun da ke bakin aiki a Masallacin Juma’a na Banki sun tare wani da ake zargin mai kunar bakin wake ne, an same shi da kayan bam.

Tsananta binciken harin Gamboru ya kai ga cafke wani ɗan ta’adda mai suna Ibrahim a Damaturu, ta hannun mafarauta tare da haɗin gwiwar OPHK.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun ragargaza Boko Haram bayan Ndume ya nemi daukin Amurka

An dawo da shi Maiduguri a ranar 29 ga Disamba domin ƙarin bincike. Ya bayyana wurin da ya ce ya ajiye jaka mai dauke da bam, amma ba a same ta ba.

Daga bisani ya amsa cewa an dasa wani bam a ƙofar masallacin, yayin da wani abokin aikinsa, Adamu, ya shiga masallacin da rigar kunar bakin wake.

Ya kuma ce an turo masu kai hari shida zuwa Maiduguri, inda uku ‘yan Maiduguri ne, sauran kuma daga Michika a jihar Adamawa.

An yi bayani game da harin Maiduguri

A baya, kun ji cewa rundunar Sojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation Hadin Kai ta tabbatar da fashewar bam a wani masallaci da ke cikin Kasuwar Gamboru a Maiduguri.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin 6.00 na yamma, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici da tashin hankali a cikin kasuwar da kewaye.

Jami’in yaɗa labarai na Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce rundunar ta samu rahoton lamarin ne a daidai lokacin da ake gudanar da sallar Magariba a masallacin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng