Abin da Shugaban NNPP a Kano Ya Ce bayan Rahoton Tsige Shi daga Kujerarsa
- Shugaban jam'iyyar NNPP na Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya yi karin haske kan rahoton cire shi daga kujerarsa
- Dungurawa ya musanta labarin korarsa daga jam’iyya, yana mai cewa har yanzu shi ne sahihin shugaba
- Ya bayyana ikirarin korar a matsayin “wasan yara” da ba shi da tushe a doka ko kundin tsarin jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano – Shugaban jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya magantu game da labarin korarsa daga shugabancin jam'iyyar.
Dungurawa ya karyata rahotannin da ke yawo cewa an kore shi daga jam’iyyar, inda ya jaddada cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban NNPP a jihar.

Source: Facebook
Dungurawa ya musanta tsige shi a shugabancin NNPP
Hakan na cikin wata sanarwa yayin mayar da martani kan ikirarin da wasu mutane daga mazabarsa suka yi na cewa sun kore shi daga jam’iyyar, cewar Tribune.
Dungurawa ya bayyana wannan mataki a matsayin marar muhimmanci kuma ba shi da goyon bayan kundin tsarin jam’iyyar.
Ya ce abin da ake kira korar tasa “wasa ne na yara”, yana mai cewa irin wadannan matakai ba su da wani tasiri a bangaren doka ko siyasa a tsarin NNPP.
Dungurawa ya yi wannan bayani ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano a daidai lokacin da ake ta yada rade-radin rikicin shugabanci da kuma sauya sheka a cikin reshen jam’iyyar na Kano.
Ya ce:
“NNPP na da ka’idoji da tsare-tsaren ladabtarwa a fili. Babu wata mazaba da ke da ikon korar shugaban jiha ba tare da bin ka’ida da kuma amincewar hukumomin jam’iyyar da suka dace ba.”

Source: Facebook
Dungurawa ya fadi shirin NNPP
Dungurawa ya kara da cewa labarin da ke cewa an tsige shi daga mukaminsa karya ne kuma mai cike da ruɗani, yana mai jaddada cewa babu wata hukuma a matakin jiha ko kasa da ta yanke shawarar cire shi.
Ya ce:
“Har yanzu ni cikakken mamba ne na NNPP kuma sahihin shugaban jam’iyyar a Jihar Kano. Babu wata shawara, a jiha ko a kasa, da ta cire ni daga mukami.”
A cewarsa, tuntubar da Sanata Kwankwaso ke jagoranta har yanzu tana gudana, kuma manufarsu ita ce tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar, cewar Punch.
Dungurawa ya ce an samu gagarumin ci gaba a wannan tsari, yana mai cewa za a sanar da ’yan jam’iyya da al’umma dalla-dalla da zarar an kammala tuntubar.
Ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu su yi hakuri, yayin da ake ci gaba da kokarin warware matsalolin cikin gida.
Jiga-jigan APC sun gana da Abba Kabir
An ji cewa ana ci gaba da samun ruɗani a Kano kan shirin da ake cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai fice daga NNPP zuwa APC.
Dan majalisa tarayya, Kabiru Alhassan Rurum ya tabbatar da cewa sun tattauna da Abba Kabir Yusuf game da sauya sheka ba tare da Rabiu Musa Kwankwaso ba.
Masana siyasa na gargaɗin cewa matakin zai sauya lissafin siyasa a Kano, tare da raunana NNPP da kawo sababbin ƙalubale kafin zaben 2027.
Asali: Legit.ng

