'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Yi Ta'asa bayan Kai Hare Hare a Kauyukan Adamawa

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Yi Ta'asa bayan Kai Hare Hare a Kauyukan Adamawa

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun hallaka bayin Allah tare da kona gidajen mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a karamar hukumar Hong
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ba a san adadin mutanen da aka kashe ba yayin hare-haren amma an gano gawarwaki har guda takwas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Wasu da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kashe mutane yayin wasu hare-haren ta'addanci da suka kai a jihar Adamawa.

'Yan ta'addan na Boko Haram sun kashe mutane takwas a wasu kauyuka uku da ke karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Adamawa
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri Hoto: @GovernorAUF
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa majiyoyin cikin gida sun tabbatar da cewa harin ya auku ne a daren ranar Litinin, 29 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Fusatattun mutane sun farmaki ofishin hukumar NSCDC a Kano, an rasa rayuka

'Yan Boko Haram sun kashe mutane

Bayan hare-haren an gano gawarwakin mutane takwas, yayin da mutane hudu har yanzu ba a san inda suke ba.

Wata majiya, da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce maharan sun kai hare-haren ne a kauyukan Zah, Kijing da Mubang, tana mai cewa lamarin ya kara tayar da hankalin jama’a da rashin tsaro a yankin, musamman a wannan lokacin bukukuwan Kirsimeti.

"Mutane da dama na ganin cewa adadin wadanda aka kashe ya fi takwas, domin an lalata gidaje da dama a yayin harin da aka kai daren ranar Litinin."
"Mutane da yawa sun gudu daga gidajensu domin tsira da rayukansu."

- Wata majiya

Me hukumomi suka ce kan harin?

Sai dai shugaban karamar hukumar Hong, Hon. Inuwa Usman Wa’aganda, ya ce abin da zai iya tabbatarwa a halin yanzu shi ne gano gawarwakin mutane takwas daga kauyukan da lamarin ya shafa.

"Eh gaskiya ne. Boko Haram sun kai hari kauyukan Mubang, Zah da Kijing da ke karamar hukumar Hong. A halin yanzu, an gano gawarwaki takwas daga wadannan kauyuka uku, kuma mutane hudu har yanzu ba a same su ba."

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kai kazamin hari a Kebbi

- Hon. Inuwa Usman Wa'aganda

Za a iya tunawa cewa a baya ma an ruwaito hare-hare a yankunan Mayo Ladde da Garaha da ke makwabtaka da yankin.

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hare-hare a Adamawa
Taswirar jihar Adamawa, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan Boko Haram

Sojoji sun ragargaji 'yan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu gagarumar nasara bayan da suka kai hare-haren sama a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, inda suka samu gagarumar nasara a kan mayakan Boko Haram.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa hare-haren sun yi sanadiyyar kawar da wasu manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram da ake dade ana nema ruwa a jallo a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng