Biki Bidiri: An Daura Auren Zaynab da Sakataren Gwamnatin Tarayya a Asirce

Biki Bidiri: An Daura Auren Zaynab da Sakataren Gwamnatin Tarayya a Asirce

  • Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya angonce da matarsa mai suna Zaynab duk da dai ba a yi wani gangamin biki ba
  • Wasu makusantan Sanata Akume sun bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Benuwai na da tsarin gudanar da rayuwarsa a cikin sirri
  • Masu sharhi kan al'amura sun ce tun da dadewa, tsohon gwamnan na gudanar da rayuwarsa bisa tsari ba tare da cakuda ta da harkokin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue, Nigeria - Rahotanni sun tabbatar da cewa an daura auren sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume da Zaynab Otiti Obanor a asirce.

Bayan labari ya bazu a kafafen sada zumunata, Sanata George Akume, ya fito ya tabbatar da cewa an daura masa aure a cikin sirri.

Sanata George Akume.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume Hoto: George Akume
Source: Facebook

An daura auren Sanata Akume a asirce

A rahoton da The Nation ta kawo, Akume ya bayyana auren da ya yi a matsayin lamari na sirri na kashin kansa wanda ba shi da alaka ga aikinsa na gwamnati ko harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

'Don Allah ka zauna a Kiristanci': Rokon matar Sanata Akume bayan ya kara aure

Majiyoyi na kusa da SGF sun bayyana cewa an jima da daura auren kuma da gangan aka shirya hakan domin nesanta auren daga ido da bakunan 'yan Najeriya.

Sun jaddada cewa daman tun asali Sanata Akume mutum ne mai son sirri a harkokin rayuwarsa na kashin kai, bai cika son bayyana wa duniya abubuwan da suka shafe shi na.

Wani babban hadimin na SGF ya ce Akume ya dade yana kebe rayuwarsa ta sirri da aikinsa na hidimar jama’a, yana mai jaddada cewa wannan ka’ida har yanzu tana nan daram.

Tsarin rayuwar sakataren gwamnatin tarayya

Masu lura da al’amura sun ce harkonin siyasar Sanata Akume sun kasance cikin daidaito da tsari, ba tare da hayaniya ba, tun daga lokacin da ya yi gwamna har zuwa matsayinsa na yanzu.

Amarya, Sarauniya Zaynab Otiti Obanor, mace ce mai aikin jin kai da fafutukar ci gaban kasa, wadda ta dade tana shiga ayyukan tallafi da suka shafi jin dadin al’umma.

Makusantanta sun bayyana cewa amaryar Akume tana gudanar da rayuwa a asirce, ta fi maida hankali wajen yin abubuwan da za su taimaki jama'a ba tare da duniya ta sani ba.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

George Akume.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume Hoto: George Akume
Source: Facebook

Wadanda suka san ma’auratan sun ce kowannensu yana da sana’a da martaba ta kansa, kuma ba su da niyyar hada lamurran rayuwarsu ta sirri da siyasa.

Wani hadimin sakataren gwamnatin Najeriya ya sake jaddada cewa har yanzu Akume yana maida hankali kacokan kan nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa, in ji Daily Post.

“Ayyukan gwamnati na ci gaba ba tare da tsaiko ba,” in ji wani jami’i, yana mai kara wa da cewa mulki da shugabanci su ne babban abin da ake bai wa muhimmanci.

An daura auren sojan ruwa, Yerima

A wani rahoton, kun ji cewa an tabbatar da cewa Laftanan Adam Muhammad Yerima ya yi aure a asirce a jihar Kaduna.

Yerima ya fara shahara ne bayan bullar bidiyon da ya hana tawagar ministan shiga wani gida da aka danganta da tsohon hafsan sojojin ruwa.

A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga Yerima da matarsa a gidan iyayenta, yayin da wani dattijo daga dangin amarya ke yi musu nasiha da addu’a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262