Malami: Kotu Ta Iza Ƙeyar Surukin Buhari da Ɗansa zuwa Gidan Yarin Kuje
- Kotu ta tura Abubakar Malami da ɗansa gidan yarin Kuje bayan sun musanta tuhume-tuhume 16 na halatta kudin haram
- Hukumar EFCC tana zargin Malami da boye biliyoyin Nairori da kuma sayen wasu manyan kadarori a jihohin Kano da Abuja
- Mai shari'a Emeka Nwite ya dage sauraron batun belin Malami, tare da sanya lokacin da za a fito da shi daga gidan yari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon babban lauyan gwamnati kuma ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN), a gidan gyaran hali na Kuje a ranar Talata.
Wannan mataki ya biyo bayan gurfanar da Malami da aka yi tare da ɗansa, Abubakar Abdulaziz Malami, da kuma wata mata, Asabe Bashir, kan zargin halatta kuɗin haram.

Source: Twitter
Kotu ta tura Malami da iyalansa gidan yari
Alƙalin kotun, Mai Shari'a Emeka Nwite, ya ba da umarnin a tsare su har zuwa lokacin da za a saurari tare da yanke shawara kan neman belin da lauyoyinsu suka yi, in ji rahoton Punch.
Malami da sauran waɗanda ake ƙara sun musanta dukkan tuhume-tuhume guda 16 da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta karanta musu.
Lauyan wadanda ake kara, Joseph Daudu (SAN), ya yi ƙoƙarin neman belin su, yayin da lauyan hukumar EFCC, Ekele Iheneacho (SAN), ya gabatar da hujjojin adawa da hakan.
Mai Shari'a Emeka Nwite ya dage zaman shari'ar bayan sauraron hujjojin kowane ɓangare domin nazarin takardun neman belin wadanda ake kara.
Zargin halatta kuɗin haram da satar N10bn
Hukumar EFCC ta yi zargin cewa Malami da iyalansa sun haɗa baki a lokuta daban-daban domin ɓoye tare da juya kuɗaɗen da aka samu ta hanyar da ba ta dace ba, waɗanda yawansu ya kai biliyoyin Nairori.
A cewar hukumar, waɗannan laifuffuka sun faru ne na tsawon shekaru, inda aka yi amfani da kamfanoni da asusun banki daban-daban wajen haramtaccen hada-hadar kuɗi.
Sannan hukumar yaki da cin hanci da rashawar, ta zargi Malami da iyalansa da sayen manyan kadarori a biranen Abuja, Kano, da sauran wurare.

Source: UGC
Zargin da ake yi wa Malami ya ja hankali
EFCC ta ƙara bayyana cewa an aikata wasu daga cikin waɗannan laifuffukan ne yayin da Malami yake riƙe da muƙamin ministan shari’a na ƙasa, a cewar rahoton The Nation.
A cewar hukumar, aikata irin wadannan laifuffuka a lokacin da yake rike da mukamin gwamnati ya saɓa wa dokokin hana halatta kuɗin haram na shekarar 2011 da 2022.
Wannan shari'a tana ɗaya daga cikin manyan shari'o'in cin hanci da rashawa da suka fi jan hankalin jama'a a wannan kakar, la'akari da muƙamin da Malami ya riƙe a baya da burinsa na zama gwamnan Kebbi.
An kai Abubakar Malami kotu
Labari ya zo mana a safiyar Talata shi ne EFCC ta gurfanar da Abubakar Malami, dansa da wani mutum daya a gaban kotun tarayya a Najeriya.
Hukumar ta jero tuhume-tuhume 16 da take wa wadanda ake zargi, wanda ya shafi almundahana a lokacin da yake babban lauyan gwamnatin tarayya.
Sai dai Malami da sauran wadanda aka gurfanar sun musanta aikata duka tuhume-tuhumen da ake masu, sai dai duk da haka za a tsare su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


