Rai Bakon Duniya: Shugaban Karamar Hukuma Ya Rasu a Yobe bayan Doguwar Jinya
- An shiga jimami a jihar Yobe bayan rasuwar daga cikin shugabannin kananan hukumomin da ake da su
- Shugaban karamar hukumar Yusufari, Alhaji Baba Abba Aji, ya yi bankwana da duniya bayan ya sha fama da jinyar rashin lafiya
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya mika sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Yobe - An yi rashi na daya daga cikin shugabannin kananan hukumomin jihar Yobe ta tarayyar Najeriya.
Shugaban karamar hukumar Yusufari ta jihar Yobe, Alhaji Baba Abba Aji, ya yi bankwana da duniya.

Source: Facebook
Wata majiya daga iyalansa ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa shugaban karamar hukumar ya rasu ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Disamban 2025.
Ciyaman ya rasu a jihar Yobe
Marigayin ya rasu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke birnin Cairo na kasar Masar.
Da yake tabbatar da rasuwar, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Jihar Yobe, Hon. Bukar Adamu, ya ce marigayin ya dade yana fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa.
Ya kara da cewa an riga an yi masa jana’iza a birnin Cairo bisa koyarwar addinin Musulunci.
"Muna mika ta’aziyyarmu ga gwamnatin jihar Yobe, karamar hukumar Yusufari da iyalan mamacin bisa wannan babban rashi. Allah Ya jikansa Ya ba shi hutu na har abada.”
- Hon Bukar Adamu
Ahmad Lawan ya yi ta'aziyya
Hakazalika, Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa, Ahmad Lawan ya mika sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayin.
Sanata Ahmad Lawan ya yi ta'aziyyar ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook.
"Cikin bakin ciki mai tsanani da cikakken mika wuya ga kaddarar Allah (SWT), na samu labarin rasuwar shugaban karamar hukumar Yusufari, Alhaji Baba Abba Aji."
"Rasuwarsa, wadda ta faru a kasar Masar a ranar Lahadi, 28 ga Disamba, 2025, ta bar babban gibi da radadi a zukatanmu da kuma daukacin mazabar Sanatan Yobe ta Arewa baki daya."
"Marigayi Alhaji Baba Abba Aji mutum ne mai kishin kasa. Rayuwarsa ta kasance cike da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da walwalar al’ummar Yusufari da jihar Yobe gaba daya."
"Mutuwarsa ba zato ba tsammani babban rashi ne ga mazabarmu, domin ya kasance abokin aiki, abin dogaro a kokarinmu na kawo ci gaba mai ma’ana ga Yobe ta Arewa."
"A wannan lokaci na bakin ciki da alhini, tunani da addu’o’ina suna tare da iyalansa na kusa. Ina rokon Allah Ya ba su hakurin jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba."
"Haka nan ina mika ta’aziyya ta ga Mai girma gwamnan jihar Yobe, Rt. Hon. Mai Mala Buni, CON, daukacin al’ummar karamar hukumar Yusufari, da kuma shugabannin jam’iyya da mambobinta baki daya."
- Sanata Ahmad Lawan

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Bauchi ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Bauchi, Birgediya Janar Abu Ali (mai ritaya) ya rasu.
Marigayi Janar Abu Ali ya shugabanci Bauchi tsakanin Satumba 1990 zuwa Janairu 1992 a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida.
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya aika da sakon ta'aziyya inda ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai hangen nesa da tsantseni wajen gudanar da al’amura.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

